A ranar Talata ne Kungiyar Kwadago ta fara yajin aikin gama-gari a Najeriya. Sai dai wannan yajin aiki ya ɗaure wa mutanen Najeriya kai matuka musamman Talaka da bai ji ba bai gani ba.
Maƙasudin shiga wannan yajin aiki dai shi ne wai don jami’an tsaro sun mammauje shugaban kungiyar Kwadago na Kasa, Ajaero a jihar Imo yayin shirya gudanar da zanga-zanga a jihar kafin zaɓe.
Bayan da aka sake shi, sai kuma ya koma wurin ƴan kungiyarsa ya tunzura su su shiga yajin aiki gadangadan.
Dubi da dalilan da suka bayar, cewa wai sai an hukunta waɗanda suka jijjibgi shugaban a Imo, kafin nan su hakura su janye yajin aikin ko kuma ƴan kasa su koka da kansu.
Sun kirkiro wasu batutuwa da ke gaban gwamnatin tarayya wanda bukatu ne da gwamnati ke dubawa kuma ta fara aiwatar su wato cika alƙawuran da suka ɗauka wa kungiyar.
Talakawa da dama da suka zanta da PREMIUM TIMES HAUSA sun yi Allah Wadai da wannan yajin aiki.
” Mu dai talaka mun zama kwallo kawai, da abinda ya shafe mu da wanda babu ruwanmu da ma wanda tsakanin shi da matarsa ne, ko kuma ma aboki da aboki, kawai don kana kungiyar Kwadago sai ku rufe kasa. Wannan abu bai dace ba, sam babu tausayi a ciki.
” Babu abinda talaka zai amfana da shi in ba tsananin azabar wahalar rayuba wanda dama da shi ya ke fama tuntuni. Odan suna da matsala da gwamnati a Imo, sai suje can su warware matsalarsu.
” An yi irin haka a Kaduna, a Kaduna aka warware matsalar, ba duka kasa ba. In ji wani mazaunin Kaduna, Nuhu Muhammed.
Ga dukkan alamu dai karara ya nuna cewa wannan yajin aiki ba don Talaka bane, ana yin sa don biyan bukatar wasu mutane ne da ban ba don matsalolin kasa ba.
Gwamnatin Tarayya ta yi kira ga NLC ta dakatar da yajin aikin ta koma teburin tattaunawa. Bayan haka kuma kotu da kanta ta hana NLC shiga yajin aikin amma sun yi biris da umurnin kotun.
Yanzu dai an shiga halin ha’ula’i a kasa baki daya musamman talakawa.
Discussion about this post