Sanata Adams Oshiomhole wanda tsohon Shugaban Ƙungiyar Ƙwadago ta Ƙasa (NLC) ne, ya yi tir da dukan da jami’an ‘yan sanda suka lakaɗa wa Shugaban Ƙungiyar Ƙwadago ta Ƙasa (NLC), a Owerri, Jihar Imo.
Oshiomhole wanda ke wakiltar Shiyyar Edo ta Arewa a Majalisar Dattawa, ya yi wannan bayani ne a ranar Laraba, lokacin da shi da wasu sanatocin APC suka je Fadar Shugaban Ƙasa, domin yi wa Shugaba Bola Tinubu murnar sake lashe da APC ta yi a zaɓen Imo da na Kogi.
Oshiomhole wanda ya yi shugaban ƙungiyar NLC daga 1999 zuwa 2007, ya ce ba ya goyon bayan a jibgi kowane ɗan Najeriya, ciki har da shugaban ƙwadago, ‘yan jarida, kowane ɗan Najeriya har da shugabannin ƙwadago,” cewar Oshiomhole.
Sai dai kuma sanatan ya ce Shugaban NLC Joe Ajaero ya tafka kuskure dangane da tsoma bakin sa da ya yi cikin siyasar jihar Imo.
Oshiomhole ya ƙara da cewa bai kamata NLC ta shiga yajin aiki kan batun saɓanin da ya faru da shugaban ƙungiyar ba.
Ya ce kamata ya yi ƙungiyar ta tunkari gwamnatocin jihohin da ba su fara amfani da tsarin Naira 30,000 a matsayin matakin ƙaramin albashin ma’aikaci ba.
Oshiomhole ya shawarci Ajaero ya nesanta kan sa daga shiga-sharo-ba-shanu cikin harkokin siyasa, kamar yadda Gwamnan Jihar Imo, Hope Uzodinma ya shawarce shi.
Maimakon haka, Oshiomhole ya shawarce shi ya tsaya tsayin daka ya kare muradun ma’aikatan Najeriya.
Discussion about this post