Masu ruwa da tsaki a fannin kiwon lafiya dake jihohin Bauchi, Jigawa da Gombe sun nuna farin cikinsu kan yadda suka ga yawan mutane sun amsa kira wajen fitow domin yin allurar rigakafin HPV.
Mahukuntan sun ce fitowar da mutane suka yi zai taimaka wajen kawo karshen cutar HPV a jihohin.
Kungiyar mai zaman kanta ‘Parenthood Organisation’ ta bayyana cewa cutar HPV cuta ce da ake iya kamuwa da ita har ta wajen jima’i.
Kungiyar ta ce wasu lokuta kwayoyin cutar kan warke a jikin mutum amma idan basu warke ba shine ke zama cutar dajin dake kama al’aurar mutum.
Yin allurar rigakafi na daga cikin hanyoyin samun kariya daga kamuwa da cutar sannan zuwa asibiti domin samun magani koda an kamu da cutar.
A Najeriya mutum sama da miliyan 1.5 kan kamu da cutar duk shekara.
Gwamnatin tarayya ta yi shirin yi wa mata masu shekaru 9 zuwa 14 allurar rigakafin cutar domin dakile yaduwar cutar.
Bisa ga tsarin da gwamnati ta yi allurar rigakafi ya fara daga watan Oktoba sannan a kammala a Nuwamba a jihohin 16 a kasar nan.
Jami’in wayar da kan mutane na ma’aikatar kiwon lafiya dake karamar hukumar Toro jihar Bauchi Malami Danjuma ya ce mutane da dama musamman daga yankin karkara sun fito domin yin allurar rigakafin.
Danjuma ya ce zuwa yanzu mata 32,350 ne suka yi allurar rigakafin daga cikin 48,000 da ake sa ran yi wa allurar rigakafin a jihar.
“Mun fara samu karancin maganin rigakafin saboda yawan mutanen da suka fito.
Ya ce mutanen sun fito saboda wayar da kai da kungiyoyin kiwon lafiya da kungiyoyin kare hakkin dan Adam suka yi.
Jami’in asusun UNICEF a jihar Bauchi Emmmanuel Emedo ya ce asusun tare da gwamnatin jihar sun yi kyakyawar shiri domin a yi wa kowa da kowa rigakafin.
Discussion about this post