Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta bayyana cewa ma’aikatan ta sun fatattaki ‘yan bindiga kuma sun ceto wasu mutum uku da suka yi garkuwa da su a jihar.
Kakakin rundunar Aliyu Abubakar-Sadiq ya bayyana cewa maharan sun kai hari a kauyen Gogalo dake karamar hukumar Jibia ranar Asabar ɗin makon jiya da yamma.
“A ranar 11 ga Nuwamba ‘yan sandan dake Jibia sun samu labarin ‘yan bindiga dauke da makamai sun kai hari kauyen Gogalo kuma sun sace wasu mutum uku.
“Nan da nan dakarun suka fara farautar maharan a cikin dazukan dake kusa da kauyen inda suka cimmasu ranar Lahadi da karfe shida na safiya.
“Dakarun sun yi bata kashi da maharan inda har suka ceto mutane uku din da aka yi garkuwa da su.
“Jami’an tsaron za su ci gaba da farautar maharan domin kamo su a hukunta su.
A jihar Kaduna kuma, Sojoji dake aiki a karkashin rundunar ‘1Division’ sun kashe ‘yan bindiga uku.
A sanarwar haka ga manema labarai kakakin rundunar Musa Yahaya ya ce dakarun sun kashe ‘yan bindigan yayin da suke sintirin a dazukan Maro zuwa Chibiya dake karamar hukumar Kajuru ranar Lahadi.
“Dakarun sun yi batakashi da wadannan mahara inda suka kashe dan bindiga daya sannan sauran sun gudu da raunin harsashi a jikinsu.
“Jami’an tsaron sun kama makamai da suka hada da AK-47 daya, bindiga kirar hannu daya, harsasai hudu da wayar hannu daya.
Bayan haka dakarun dake karkashin rundunar ‘1 Division’ da ‘Operation Whirl Punch’ a ranar 10 ga Nuwamba sun kashe dan bindiga daya sauran sun gudu da raunin harsashi a jikinsu a kauyukan Kawara da Filin Jalo dake karamar hukumar Igabi.
“Dakarun sun kama bindiga AK-47 daya da harsasai 30, babur daya da wayar hannu kirar ‘Techno’ daya.
Yahaya ya ce dakarun sun Kuma kashe dan bindiga daya yayin da suke sintirin a dazukan dake kauyukan Mai-Kulu, Gwanda, Rafin Gora, Funtua Badadi da Kabawa a karamar hukumar Birnin Gwari.
“Jami’an tsaron sun kama karamar rediyo kirar Boafeng daya da babur daya.
Discussion about this post