A ranar Juma’a ne aka yi artabu tsakanin jami’an rundunar Sojin Saman Najeriya da na hukumar EFCC a ofishin hukumar dake Kaduna inda sojojin suka yi kokarin kutsawa cikin ofishin su fiddo wasu jami’an su da EFCC ke tatsare da a ofishinta.
Kakakin EFCC, Dele Oyewale ya bayyana cewa an kama Sojojin su hudu a wani gidan cin abinci da ke Barnawa ranar Litinin.
Sai dai bayan haka kuma sai wasu daga cikin sojojin da ke wurin lokacin da aka yi kamen suka je suka shirya, suka yi wa ofishin EFCC din diran mikiya dauke da makamai domin kokarin fidda abokan su da ke tsare a ofishin.
Ba su samu daman iya fidda su ba sai suka koma a wannan rana.
Oyewale ya kara da cewa tun daga wannan rana mahukuntan sojojin saman suka fara tattaumawa da EFCC domin a saki sojojin.
Amma kuma ana haka ne sai wasu sojojin suka sake afkawa ofishin EFCC din wannan karon kamar sun fito yaki. A haka dai dakarun EFCC suka hana su shiga ginin ofishin.
A karshe dai, Oyewale ya ce sun daidaita da mahukuntan sojojin saman sun saki masu laifin.
Ana zargin sojojin da tafka gagarimar harkalla a yanar gizo, wanda EFCC ta bi bibiyan su har suka shiga hannu.
Discussion about this post