Da Sunan Allah, Mai Rahama, Mai Jinkai
Assalamu Alaikum
Ya ku ‘yan uwana al’ummar Najeriya! Don Allah wane mutum ne mai hankali, mai ilimi, mai basirah, tunani da hangen nesa, da baya son kasarsa da yankinsa da jiharsa da garinsa, wanda aka haife shi a cikinsa, ya rayu tun yana jariri (jinjiri), ya taso a cikinsa, yayi samartaka a cikinsa, ya girma a cikinsa, kuma ya rayu a cikinsa?
Wanene a cikinmu zai manta da irin rayuwa mai dadi, ta zaman lafiya da kwanciyar hankali, da ci gaba, da farin cikin da yayi a lokacin da ake zaune lafiya a kasar mu Najeriya?
Ya ku ‘yan uwa, wallahi babu mai nufin kasar sa da sharri, babu mai cin amanar kasar sa, babu wanda zai cuci kasar sa, ko a hada kai da shi a cuci kasar sa. Ko ya aikata aikin da zai zama sandiyyar rugujewar kasar sa, ko ya zalunci al’ummar jiharsa da yankinsa, sai wanda yake wawa, dabba, jahili kuma dibgagge!
Ko shakka babu, lallai in dai har mun kasance masu hankali ba dabbobi ba, to dole ne mu so kasar mu, mu kaunace ta, muyi mata Addu’a da fatan alkhairi. Kuma dole ne muso jihohinmu da garuruwanmu, da yankunanmu, kuma muyi alfahari da jinginuwa zuwa ga re su, kuma mu tashi tsaye wurin kare su, da daga darajarsu da martabarsu; tare da yin fito-na-fito da yakar duk wani mai kokarin bata su.
Wajibi ne kuma dole a gare mu, mu tashi tsaye, mu kare kasarmu da jihohinmu, da garuruwanmu da yankunanmu daga miyagu, masu kokarin mayar da mu baya a koda yaushe. Dole mu roki Allah ya tsare muna garuruwanmu da jihohinmu da kasar mu baki daya, daga dukkan sharri da fitina da tashe-tashen hankula da kuma hare-haren ‘yan ta’adda da dukkanin nau’ukan miyagu, wadanda basu nufin kasarmu da jihohinmu da alkhairi.
Saboda muhimmancin addu’a, da kasancewar ta babbar ibadah daga cikin ibadodin da Allah ya wajabta a kan mu, shi yasa muka yanke shawarar gabatar da addu’oi muhimmai, domin Allah ya kare muna garuruwanmu da jihohinmu da kasar mu baki daya; kuma da nufin Allah Madaukaki ya dauke muna bala’o’i da rikice-rikice, da damuwoyin da suke addabar kasarmu da jihohinmu da garuruwanmu.
‘Yan uwa masu daraja! Bayan godiya ga Allah da salati ga fiyayyen halitta, Annabi Muhammad (SAW), muke cewa:
Allahummah Ya Hafiz, ya mai kariya, ka kare kasarmu da jihohinmu da garuruwanmu da al’ummominmu baki daya daga fitinar rashin tsaro; ya Allah ka azurta mu da zaman lafiya da aminci, don tsarkin sunayenka!
Ya Allahu, ya Karim, don son mu da kaunar mu ga fiyayyen halitta, Annabi Muhammad (SAW), ka sanya garuruwanmu da jihohinmu da yankunanmu da kasar mu Najeriya, su zama wurare masu aminci, wuraren zaman lafiya da ci gaba.
Ya Allah, muna tawassali da kyawawan ayukkan mu, ka kare kasarmu da jihohinmu da yankunanmu da garuruwanmu daga dukkan sharri da dukkan abun ki, ya ubangijin halittu.
Ya Allah, ka sanya garuruwanmu da yankunanmu da jihohinmu da kasarmu su zama abun so da kauna ga jama’arsu da sauran al’ummar duniya baki daya.
Ya ubangijinmu Allah, ya mafi alkhairin masu kariya, ka tsare garuruwanmu da yankunanmu da jihohinmu da kasar mu daga dukkan abun kyama, ka sanya su a karkashin kulawarka da tsaron ka na har abada, ya mafi jinkan masu jinkai.
Ya Allah, ya mai azurtawa, ka azurta kasar mu da jihohinmu da garuruwanmu da yankunanmu da arziki mai albarka daga gare ka. Ya Allah, ka sa su zama wuraren da ake tsayar da adalci, wurare masu cike da alkhairi.
Ya Allah, mu ‘yan kasar, ka sanya mu mu zama ‘yan kasa nagari, masu tsoron Allah, masu tausayi da imani, masu kadaita Allah a cikin bautarsa, masu son kasar su, so na hakika.
Ya Allah, ka dawwamar da ni’imominka a cikin mu, ka azurta mu da zaman lafiya, da walwala da jin dadi da kaunar juna.
Ya Allah, muna rokon ka, ba don halin mu ba, ka tausaya muna, ka jikan mu, ka sanya yankunanmu da garuruwanmu da jihohinmu da kasar mu Najeriya, su zama wurin zaman lafiya da jin dadi. Ka kare su da kariyar ka daga dukkan damuwa da masifa.
Ya Allah, ya mafi karfin masu karfi, ka sanya yankunanmu da jihohinmu da garuruwanmu da kasar mu Najeriya, su kasance wuraren aminci, da ci gaba, da zaman lafiya.
Ya Allah, ka tsare, kuma ka kare yankunanmu da garuruwanmu da jihohinmu da kasar mu daga dukkan sharri da fitina, na fili da na boye, wadanda muka sani da wadanda bamu sani ba. Ka kare su daga dukkan hare-haren miyagu da ‘yan ta’adda ya ubangijin halittu.
Ya Allah, ka sanya yankunanmu da garuruwanmu da jihohinmu da kasar mu su zama garuruwan alkhairai da albarka da aminci da taimakon juna da ‘yan uwantaka da hadin kai; ya Allah ka kare al’ummomin mu daga dukkan sharri, wanda zai kai mu ga dawwamammen zaman lafiya da ci gaba.
Ya Allah, ya mai azirtawa, ka azurta garuruwanmu da yankunanmu da jihohinmu da kasar mu da aminci da tabbatuwa. Ka sanya su su zama wuraren daukaka da buwaya da girman matsayi da karimci da muhibbah.
Ya ubangijin mu, ya mamallakin komai da kowa, ya mai tsarki, mun bada kulawar garuruwanmu da yankunanmu da jihohinmu da kasar mu da dukkan al’ummomin mu a gare ka. Ka sanya zaman lafiya da aminci da walwala da jin dadi a gare su. Ka amintar da su dare da rana da kowane lokaci. Ka tsare su da tsaron ka daga dukkan sharri da fitina da munanan ayukka. Ka kare manyan mu da kananan mu ya ubangijin halittu baki daya.
Ya Allah, ya mafi kariyar masu kariya. Ya mafi tsaron masu tsaro. Ka tsare garuruwanmu da yankunanmu da jihohinmu da kasar mu da dukkan al’ummomin mu, daga dukkan sharrin masu kai hare-hare da dukkan barayi da kowane nau’i na ‘yan ta’adda. Dukkan mai nufin mu da alkhairi ka taimake shi, dukkan mai nufin mu da sharri, idan mai shiryuwa ne, ka shiryar da shi, idan ba mai shiryuwa bane kayi muna maganinsa.
Ya Allah, ka kare kasar mu da jihohinmu da yankunanmu da garuruwanmu daga dukkan wani nau’in cututtuka da rashin lafiya. Ka yaye muna dukkan damuwa da kowace irin cutarwa.
Ya Allah, duk mai nufin kasar mu da jihohinmu da yankunanmu da garuruwanmu da al’ummomin mu da sharri, ka shagaltar dashi ga kansa. Ka sanya halakar sa a hannunsa. Ka tozartar da duk wani kulle-kullensa da makirce-makircensa, ya mafi karamcin masu karamci.
Ya Allah, ka kare kasarmu mai girma da daraja da jihohinmu da garuruwanmu da yankunanmu daga dukkan wani hari na barayi da ‘yan ta’adda. Ya Allah ka nesanta su daga sharrin dukkan wani masharranci, wanda baya nufinsu da alkhairi, wanda kullun kokarinsa ya cutar da mu. Ya Allah, ka kare mu daga zaluncin azzalumai, ya mafi kariyar masu bada kariya. Ya mafi jinkan masu jinkai. Ya mafi tausayin masu tausayi.
Ya Allah, ka daga tutar addininka na Musulunci ta zama madaukakiya. Ka daga tutar kasar mu Najeriya taci gaba da tabbatuwa akan girma da daraja. Kar ka bayar da dama ga mai hasada da mugu da azzalumi da marasa mutunci, marasa tausayi da imani ya jagorance ta, kuma ka tabbatar wa kasar mu da maysayinta madaukaki a duniya ya ubangijin halittu.
Ya Allah, a wannan rana, muna neman tsarin ka da kiyayewar ka. Ka mai do muna da amincin mu da zaman lafiyar mu da tattalin arzikin mu. Kar ka tozarta mu a idon duniya ya mafi kyautar masu kyauta. Kar ka bayar da dama da iko da karfi, ga masu tada-zaune-tsaye, wadanda basu son zaman lafiya, masu tozarta matayen mu da al’ummomin mu ya Allah. Muna rokon ka, ka azurta mu da dawwamammen zaman lafiya da aminci. Ka kare mu daga dukkan sharri da dukkan wani abun ki, abun tsoro. Ka tsare garuruwanmu da yankunanmu da jihohinmu da kasar mu daga dukkan sharri da bala’i. Ka kare dukkan jama’ar mu, kuma kasa muci nasara akan dukkan azzalumai da masharranta da miyagu da makirai.
Ya ubangijin mu, ya Allah, muna rokon ka, ka taimaki mutanen Gaza da dukkan jama’ar kasar Falasdin, da sauran kasashen musulmi, da kasar mu Najeriya. Ka kare su daga dukkan damuwa da wahala. Ka sanya su su zama yanki mai cike da zaman lafiya da aminci. Kuma ka sa duniya ta kaunace su ya mafi rahamar masu rahama.
Ya Allah, ka taimaki rundunonin mu da dukkan jami’an tsaron mu. Ka kare su daga dukkan sharrin masu sharri. Ka taimake su akan dukkan wani azzalumi, wanda baya nufin mu da kasar mu da jihohinmu da yankunanmu da garuruwanmu da alkhairi. Ya Allah ka basu nasara, ka taimake su, kayi amfani da su wurin samar da zaman lafiya da tsaro a tsakankanin mu.
Ya Allah, ka taimaki dukkan shugabannin mu wadanda suke nufin mu da kasar mu da jihohinmu da yankunanmu da garuruwanmu da alkhairi. Ka datar dasu da dukkan alkhairanka. Ka taimake su wurin tafiyar da shugabancin al’ummomin su.
Ya Allah, ka tsare dukkan iyakokin kasar mu ta kowane gefe. Ka tsare su ta gabas da yamma kudu da arewa. Ka kare mu da kariyar ka daga dukkan sharri da dukkan makircin makiya. Ka kare mu da kariyar ka ya wanda bacci da gyangyadi da angaje basu kama shi, ya ubangijin halittu.
Ya ubangijin mu mai karimci, muna rokon ka a wannan rana, ka kare muna addinin mu da imanin mu da akidar mu. Ka tabbatar damu cikin dawwamammen zaman lafiya da aminci da tsaro da walwala da jin dadi da kwanciyar hankali da wadata, ya mafi karimcin masu karimci.
Ya ku ‘yan uwana masu daraja, ya ku bayin Allah, ku sani, lallai Addu’a ibadah ce mai girma, kuma Allah yana son masu rokon shi, don haka ya zama tilas, dole kuma wajibi, mu tashi tsaye, tsakanin mu da Allah, muyi wa kasar mu Najeriya da jihohinmu da yankunanmu da garuruwanmu Addu’a, a kowane hali da yanayi muka samu kan mu a ciki. Domin wallahi bamu da kasar da ta wuce Najeriya. Idan tayi kyau kuma ta gyaru, to dukkanin mu zamu ji dadi. Idan kuma ta baci ko ta lalace, to dukkanin mu ne zamu ci gaba da shan wahala, Allah ya kiyaye, amin.
Kuma shugabanni, suma dole muyi masu Addu’a da fatan alkhairi. Domin sune direbobin da Allah ya damka tukin wannan kasa tamu da jihohinmu a hannunsu. Rashin hankali ne da hauka da tabewa, kaga mutum yana zagi da la’anta da cin mutuncin shugabanni.
Ta yaya za’ayi idan ba hauka ba, kana cikin mota, kuma ka rinka rokon Allah yasa direban motar ya samu matsala? Kaga ko hankali ba zai yarda da wannan ba balle addinin mu na Musulunci mai girma.
Ya ubangijin mu, ya mai jinkan bayinsa, muna rokon tausayinka da rahamar ka a wannan rana. Muna rokon gafararka. Muna rokon falalarka. Ka sanya al’ummar kasar mu Najeriya su zama masu tsoron ka. Ka daukaka darajarsu duniya da lahira, ya ubangijin halittu.
Ya Allah, a wannan rana, muna rokon ka, ka tsare garuruwanmu da yankunanmu da jihohinmu da kasar mu da tsaron ka da kariyar ka.
Ya Allah, ya mai iko akan komai, muna rokon ka, ka karfafa mu da karfin ka, ta yadda ba wani azzalumi da zai buwaye mu. Ka azurta mu da himma madaukakiya ta yadda ba zamu kasa tunkarar duk wani mugu ba. Ka bamu juriya, hakuri da jajircewa, da karfin hali, ta yadda zamu iya tunkarar dukkan wani azzalumi, wanda baya son kasar mu da jihohinmu da yankunanmu da garuruwanmu su zauna lafiya.
Ya Allah, ya mafi kyautar masu kyauta. Ya mai azurta bayinsa. Ya mai ciyar da bayinsa. Ka azurta kasar mu da jihohinmu da yankunanmu da garuruwanmu da dukkan alkhairanka masu yawa. Ka sanya su su zama wurin ci gaba da hadin kai da kwanciyar hankali. Ka tsare su daga hasadar masu hasada. Ka tsare su daga sharrin masu sharri. Ka kare su daga makircin masu makirci.
Ya Allah, a wannan rana, muna rokon ka da sunayenka kyawawa, da siffofinka madaukaka, ka tsare garuruwanmu da yankunanmu da jihohinmu da kasar mu, wadanda suke abubuwan kaunar mu, daga dukkan sharri. Ya Allah, ka taimaki al’ummomin mu, ka taimaki rundunonin mu da jami’an tsaron mu. Ka gafarta muna da dukkan ‘yan uwanmu da magabatan mu, wadanda suka sadaukar da rayukansu domin Allah, wurin kare wannan kasa da al’ummarta. Wadanda suka sadaukar da dukkan abunda suka mallaka, na ilimi da dukiya da karfi da lokaci wurin ci gaban kasar su da al’ummomin su. Ya Allah, Ka tozarta tsare-tsaren duk wani mai yi muna makirci da zagon kasa, ya zal-jalali-wal-ikram.
Ya Allah, kar ka nuna muna wani abun ki a kasar mu, wanda zai bakanta muna rai. Ka taimake mu akan aikata alkhairi ga kasar mu a koda yaushe. Ka sanya soyayya da kauna da taimakon juna da ‘yan uwantaka da hadin kai a cikin zukatan mu da rayuwar mu baki daya. Ka sanya mu mu zama masu yin hidima ga addinin ka da kasar mu da al’ummomin mu har abada.
Ya Allah, ya mafi tsaron masu tsaro, ka tsare garuruwanmu da yankunanmu da jihohinmu da kasar mu da dukkan al’ummomin mu daga dukkan sharri da mummunan abu da bakin ciki.
Ya Allah, ka kare shugabannin mu, masu son mu, masu kaunar mu, masu nufin alkhairi a gare mu da kasar mu, ka tsare su ya mafi jinkan masu jinkai. Ka datar da su da dukkan alkhairan ka. Ka albarkaci rayuwarsu. Kayi masu kyakkyawan sakamako duniya da lahira.
Ya Allah, ka taimake mu da masu mulkin mu da jihohinmu da yankunanmu da garuruwanmu da kasar mu. Ka kare mu daga dukkan damuwa da bakin ciki da dukkan sharri da fitina. Ka tausaya muna da tausayinka. Ka nesanta mu daga dukkan fitina, ta fili da ta boye, wadda muka sani da wadda bamu sani ba. Ka rayar da mu rayuwa mai kyawo ya mafi jinkan masu jinkai.
Ya Allah ka gafarta muna, mu da iyayenmu da kakanninmu da dukkan magabatanmu, da dukkan wadanda suka riga mu da kyautatawa. Ya Allah ka bamu lafiya, ka kare mu daga dukkan cuta da ciwo da rashin lafiya. Ka kasance tare da mu a koda yaushe. Ka taimake mu kar ka taimaki makiyanmu akan mu. Ka sa albarka a cikin dukkan abunda muka tunkara a rayuwar mu.
Ya Allah, ya mafi karamcin masu karamci, ka shiryar da mu da shugabannin mu wadanda suke kaunar mu kuma suke nufin mu da kasar mu da alkhairi akan dukkan abunda akwai alkhairi a cikinsa. Ka kare su da mu daga dukkan sharri. Ka sanya mu da su mu zama mabudin alkhairi, makullin sharri. Ka tashe mu da su a cikin tawagar Annabawa da siddiqai da shahidai da salihan bayi a cikin aljannarka ta ni’imah.
Ya Allah, ya mafi kyautar masu kyauta, ka sanya kasar mu ta kasance kasa mai cike da tsoron Allah da imani da albarka. Ka karfafa jama’ar kasar mu da masu mulkin mu da dukkan jagororin mu, ka dora hannayen mu akan aikata aiki nagari. Ka sanya kasar mu ta zama kasa mai girmama addinin ka, ya mai girma, mai rahama, ya ubangijin halittu baki daya.
Ya Allah, ka bamu abu mai kyau a duniya, kuma ka bamu abu mai kyau a lahira, kuma ka kare mu daga azabar wuta.
Ya Allah, Ka shiryar da mu da zuri’ar mu baki daya akan tafarki madaidaici. Ka kare mu daga dukkan damuwar duniya da ta lahira.
Ya Allah, muna rokon ka, ya Allah, ya abun nufi da bukata, wanda bai haifa ba kuma ba’a haife shi ba, wanda bai da wani tamka a gare shi, ka gafarta muna zunuban mu, domin lallai kai mai gafara ne, mai jinkai.
Ya Allah, muna rokon ka falalarka da rahamar ka, wadanda babu mai mallakar su sai kai kadai.
Ya Allah, muna neman tsarinka daga rinjayar bashi, da rinjayar makiyi, da shammatar makiya!
Ya Allah, muna neman tsarinka daga talauci, da yunwa, da rashi, da kaskanci; kuma muna neman tsarinka kar ka bari a zalunce mu, mu kuma kar ka bari mu zalunci kowa.
Ya Allah, muna neman tsarinka daga muguwar rana, da sharrin dare, da lokaci mai cike da hadari, da mugun aboki, da mugun makwabci.
Ya Allah, muna neman tsarinka daga yunwa, da ha’incin maha’inta.
Ya Allah, ka sanya mu mu zama masu yawaita godiya a gare ka, masu yawan ambatonka, masu kyautata bauta a gare ka.
Ya Allah, ka azurta mu da arzikinka, ka suturta mu da suturarka.
Ya Allah, muna neman tsarinka daga gushewar ni’imarka, da rashin lafiya, da saukar azabarka, da fushin ka a gare mu.
Ya Allah, duk wanda ka bai wa shugabanci, sai ya kuntatawa bayin ka, ya Allah ka kuntata mashi. Duk wanda ka bai wa shugabanci, sai ya tausayawa bayin ka, ya Allah ka tausaya mashi.
Ya Allah, muna neman tsarinka daga sharrin abunda muka aikata da wanda bamu aikata ba.
Ya Allah, rahamar ka muke nema, kar ka bar mu da kawunanmu daidai kyaftawar ido. Ka kyautata dukkanin al’amurran mu.
Ya Allah, muna neman tsarinka daga cutar kuturta. Da cutar hauka da tabuwar hankali, da dukkan nau’in cututukka.
Ya Allah, lallai mun zalunci kawunanmu zalunci mai yawa, kuma babu mai gafarta zunubai sai kai, ka gafarta muna da gafara daga gare ka, ka tausaya muna, lallai kai mai yawan gafara ne, kuma mai jinkai.
Ya Allah, muna neman tsarinka daga damuwa; ka yaye muna dukkan damuwa, da bakin ciki, da kasawa, da kasala, da tsoro da rowa da matsalar bashi, da rinjayar makiya.
Ya Allah, ka azurta mu da cin halal, ka kare mu daga cin haram, ka wadata mu da falalarka.
Ya Allah, ka bamu lafiya a jikin mu, ka bamu lafiya a cikin jin mu, ka bamu lafiya a ganin mu da idon mu; ya Allah muna neman tsarinka daga kafirci da talauci; muna neman tsarinka daga azabar kabari.
Amin ya mafi tausayin masu tausayi, ya ubangijin halittu.
Wassalamu alaikum wa rahmatullah wa bara ka tuh.
Dan uwanku, Imam Murtadha Muhammad Gusau, ya rubuto daga Okene, Jihar Kogi, Najeriya. Za’a iya samun sa a lambar waya kamar haka: 08038289761.
Discussion about this post