Tsohon Shugaban Ƙungiyar Lauyoyi ta Ƙasa (NBA), Olumide Akpata, ya ce duk inda ka ga an samu mai shari’a nagari a ƙasar nan, to dace ne kawai, amma shi ma ɗin ba ta hanyar da ta dace aka naɗa shi ba.
Akpata ya ce tsarin da ake bi ana naɗa masu shari’a a Najeriya, a lalace ya ke, dalili kenan martabar fannin shari’a ba shi da wata daraja yanzu a Najeriya.
Tsohon Shugaban na NBA, ya bayyana haka lokacin da ya ke jawabi wurin Taron Ƙungiyar Lauyoyi na Duniya, a Paris, babban birnin Faransa.
Da ya ke jawabi a gaban mahalarta taron, Akpata ya ce matsayin Najeriya mai mafi yawan ɓaƙar fata a duniya, ƙasar na fama da wani “kamun-kazar-kuku” da gungun ‘yan siyasa suka yi wa fannin shari’a.
Ba shi kadai ya yi irin wannan kukan ba, shi ma farfesan shari’a, kuma tsohon Shugaban Hukumar Kare Haƙƙin Ɗan Adam (NHRC), Chidi Odinkalu ya watsa wannan bayani a shafin sa na Tiwita a ranar Juma’a.
An nuno Akpata a cikin wasu gajerun faifan bidiyo biyu ya na nuna damuwa kan yadda masu mulki suka ƙudundune fannin shari’a, su ka cusa aljifan su.
Akpata wanda ta yi Shugaban NBA daga 2021 zuwa 2022, ya bayyana yadda tsarin naɗa alƙalai ya lalace a Najeriya.
“Inda duk ka ga an naɗa alƙali nagari, to sa’a ce kawai aka yi, amma ba bisa cancanta aka zaɓe shi ba. Saboda tsarin da ake bi ana naɗa alƙalai gurɓattacce ne.”
A matsayin Akpata lokacin da ya ke Shugaban NBA, ya na cikin Majalisar Kula da Alƙalai ta Ƙasa (NJC). Wannan majalisa ce ke naɗa masu shari’a a manyan kotunan Najeriya. Kuma ita ce ke ladaftar da alƙalan da aka kama da laifi.
“Lokacin da ina Shugaban NBA, na gano yadda masu mulki ke ƙudundune fannin shari’a, su na jefawa aljifan su. Hakan ya lalata tasirin tsarin shari’a sosai a ƙasar nan. Kuma su dai kam su na cin ƙazamar riba da irin wannan tsiyar da suke tsulawa.”
‘Alƙalan Ƙarambosuwa A Wasu Kotunan Najeriya’ – Akpata
“Wato wasu alƙalan da ake naɗawa wai masu shari’a, gaskiya magana wurin bai cancance su ba, kuma naɗa su zubar ƙimar fannin shari’a ne.”
Ko kwanan nan shi ma Odinkalu ya fito ya yi taratsi kan naɗa wasu alƙalai, irin su Babban Jojin Najeriya, Olukayode Ariwoola da Shugaban Kotun Ɗaukaka Ƙara da sauran su.
Ya soki naɗe-naɗen da suka yi wa ‘ya’yan su da matan su a matsayin alƙalai. Da yawan ‘ya’yan wasu alƙalan da suka yi ritaya da waɗanda ke kan aiki, su ma an naɗa su alƙalai a ƙasar nan.
Akpata ya koka kan yadda gwamnoni ke yadda suka ga dama da alƙalan jihohi, ta hanyar hana su haƙƙin su da dakar ƙasa ta wajabta a yi masu.
Discussion about this post