Gwamnan Kaduna, Uba Sani ya yi wa waɗanda suka yi nasara a gasar karatun Kur’ani da aka yi a Kaduna kyautar kujerun Makka kowannen su
Hakan na kunshe na a jawabin sa gwamnan yayi a wajen taron rufr gasar karatun Kur’anin wanda aka yi a Kaduna.
Gwamna Sani ya ce na miji da macen da suka zarra, za su je aikin Hajji na 2024 karkashin gwamnatin jihar.
Bayan haka gwamnan ya yi kira da a rika maida hankali wajen koya wa yara darussan dake cikin Alkur’ani domi su samu fa’idodin su da ma sauran jama’a baki ɗaya.
Da yake magana game da matsalolin da aka samu a aikin hajjin bara musamman mahajjatan jihar Kaduna, gwamna Sani ya ce a karkashin mulkin sa ba za a samu irin haka ba.
” Za mu duba muga a ina aka samu matsalolin sannan kuma da tabbatar da irin haka bai sake faruwa ba musamman wurin maganar abincin ci ga mahajjata.
A karshe gwamnan ya fallasa wasu da suka tunkare shi wai a basu kwangilar ciyar da mahajjata a lokacin Hajji mai zuwa. Ya gargaɗe su da su ji tsoron Allah a ayyukansu cewa idan suka zalunci mutane, Allah na ganin su kuma addu’ar wanda aka cuta karɓaɓɓiya ce.
Da ya ke tofa albarkacin bakin shi a wurin taron, shugaban ƙungiyar Izala, ta kasa Sheikh Bala Lau ya jinjina wa gwamna Uba Sani, yana mai cewa jihar Kaduna ta yi sa’a na samun gwamna mai tausayi wand hannun sa a buɗe yake wajen kyauta da taimakon mabuƙata.
Sannan kuma ya yaba masa bisa ayyukan ci gaba da ya bijiro da su a faɗin jihar domin mutanen jihar.
Discussion about this post