Jami’an tsaron da aka tabbatar ‘yan sanda ne sun tsare Olayinka Braimoh, ɗan takarar gwamnan Kogi a ƙarƙashin jam’iyyar AA.
Kakakin Yaɗa Labaran ɗan takarar mai suna Yakubu Musa, ya shaida wa wannan jarida cewa an kama Braimoh a Ƙaramar Hukumar Kabba Bunu, bisa zargin an samu takardun kamfen a cikin motar sa.
Ya ce hankalin su ya tashi bayan sun daina jin ɗuriyar ɗan takarar da sauran ‘yan rakiyar sa da jami’an tsaron da ke kare shi.
Ya ce bayan sun yi magana da shi da safe, daga nan sai wayoyin sa da na jami’an tsaron sa da na sauran hadiman da ke tare da shi, duk su ka kasance a kashe.
Musa ya ce su kuma samu labarin cewa an tattara har da jami’an tsaron da ke tare da shi da na hadiman sa duk su ma a kashe.
Wannan lamari a cewar sa ya faru tun ma kafin Braimoh ya jefa ƙuri’ar sa.
Musa wanda ya ke magana shi a lokacin ya na Ƙaramar Hukumar Ijumu, ya ce sai da yamma aka saki Braimoh, wanda aka tsare tun da safiya, amma har zuwa Magaribar ranar Asabar ɗin da aka kama shi ɗin ba a saki jami’an tsaron sa ba.
Discussion about this post