Darajar Naira na ci gaba da zubewar, yayin da Dala da manyan kuɗaɗen waje irin su Yuro da Fam na Ingila ke ci gaba da tsala wa Naira bulaloli a tsakiyar kasuwar hada-hadar musayar kuɗaɗe.
Faɗuwar darajar Naira na haifar da tsadar kayayyakin da ake shigowa da su daga waje, kama daga kayan masarufi, abinci ko kayayyakin ayyukan yau da kullum, na’urori da sauran su.
A ranar Alhamis dai an sayar da Dala 1 kan Naira 841.14 a bankuna kan farashin gwamnati.
Amma kuma an sayar da ita Naira 1,132.00 a kasuwar hada-hadar ‘yan canji.
Hakan kuwa ya nuna ƙara faɗuwar darajar Naira ɗin, idan aka kwatanta da yadda ta ke a ranar Laraba, inda aka sayar da ita Naira 1140.
A cikin ƙasa jama’a na fama da matsin rayuwa da tsadar kayan abinci da ta kayan amfanin yau da kullum, tun bayan janye tallafin fetur da sabuwar gwamnatin Bola Tinubu ta yi, a ranar da aka rantsar da shi.
Ko a ranar Alhamis sai da Ministan Harkokin Kuɗaɗe Wale Edun ya bayyana cewa Najeriya ba za ta gaba da ciwo bashi domin gudanar da ayyukan raya ƙasa ba a cikin kasafin 2024.
Bashin da ake bin Najeriya a ƙididdigar da Ofishin Kula da Basussuka, DMO ya yi a ƙarshen Satumba, ya ce kuɗin sun haura Naira tiriliyan 87.
Discussion about this post