Shugaban Kasa Bola Tinubu ya mika ta’aziyyar sa ga iyalan marigayi Usman Baba-Pategi, da aka fi sani da ‘Samanja’.
Tinubu ya ce an yi rashi a Najeriya.
” Samanja mutum ne da ya sadaukar da kansa wajen gina Kasa sannan mutum ne mai kishin kasa da al’umma. Ya bada gudunmawa matuka waje haɗin kan kasa.
” Ina addu’a Allah ya ji ƙansa ya sa Aljannah ta zamo makoman sa, Amin.
Samanja ya rasu yana da shekaru 84 a duniya.
Discussion about this post