Shugaban Ƙasa Bola ya gana da ɗaya daga cikin shugabannin Bankin Musulunci, wato ‘Islamic Development Bank’ a birnin Makka, Saudi Arebiya.
Sun yi ganawar ce a lokacin wannan ziyara ta taron da ya halarta a ƙasar. Kuma maƙasudin taron shi ne tattauna buƙatun hanyoyin zuba jari a Najeriya, domin bunƙasa ayyukan raya ƙasa.
A ganawar wadda Tinubu ya yi da Mataimakin Shugaban Bankin Musulunci, mai kula da ƙasashe, Mansur Muhtar, a Makka, ya shaida masa cewa cewa Najeriya na da gagarumin giɓi sosai a fannin harkokin tashoshin ruwa, makamashi, sai kuma ɓangaren kayayyakin bunƙasa noman zamani.
A nan sai Tinubu ya shaida masa cewa dukkan waɗannan ɓangarori uku su na da matuƙar buƙatar zuba jari.
“Muna da wawakeken giɓi a harkokin tashoshin ruwa, makamashi da ɓangaren kayan noma na zamani waɗanda za su sanar da wadataccen abinci a ƙasar mu.”
Cikin sanarwar da Kakakin Yaɗa Labarai na Tinubu, Ajuri Ngelale ya fitar, shugaban ƙasar ya shaida wa Bankin Musulunci cewa Najeriya na matuƙar buƙatar zuba jari daga ɓangaren bankin.
A na sa jawabin, Muhtar ya tabbatar wa Shugaba Tinubu cewa IDB ya ƙudiri aniyar tabbas zai goyi bayan Najeriya.
“Shugaban Ƙasa, muna sane da cewa ka gaji ƙalubale masu yawa. Mun kuma gamsu da yadda ka ɗauki tsauraran matakai a cikin gaggawa. Saboda haka a shirye muke mu yi aiki tare da kai. Mun shirya goyon bayan duk wani babban aikin bunƙasa tattalin arzikin Najeriya.
“Mun yarda cewa, idan Najeriya ta yi nasara, to Arewa ce ta yi nasara. To kuma duniya na matuƙar buƙatar Afrika ta yi nasara,” inji Muhtar.
Discussion about this post