Kungiyar kwallon kafa ta Luton ta kusa ta sa Liverpool ta kwashi kashinta a hannuna wasan Premier League da aka buga a karshen wannan mako.
Wasan da aka buga shi da yammacin Lahadi ya yi kamar za a yi wa Luton ambaliyar kwallaye ne a ragar ta sai wankin hula ya nemi kai Liverpool dare.
Ana gab da a ƙarƙare wasan babu ci sai Luton ya birkita wa Liverpool lissafi, ta goge mata hadda gaba ɗaya. Ɗan wasanta Chong ya jefa kwallo a ragar Liverpool.
Hankalin Liverpool ya tashi, ƴan wasanta suka fusata, kowa sai farmaki ya ke kai wa Luton, amma kwallo ya gagara shiga ragar Luton.
Abinka da kwararre, babu irin lissafin da Liverpool ba ta yi ba, da dabaru daban-daban amma inaaa.
Da dai abin ya yi zafi, Diaz a minti 90+5 ya sammaci Lotun ya samu ya farke wa kungiyar sa wannan kwallo daya da aak saka a ragarsu.
An tashi wasa 1-1.
Liverpool tana na huɗu da maki 24, ita kuma Luton na 17 da maki 6.
Discussion about this post