Kungiyar masu fama da ciwon siga na Najeriya ta bayyana cewa mutum miliyan 11.2 ke fama da ciwon a kasar nan.
Shugaban kungiyar Alkali Mohammed ya sanar da haka a taron ranar ciwon ta duniya da aka yi a Abuja ranar Litinin.
Ranar ciwon siga na duniya rana ce da UN ta kebe domin dakile yaduwar ciwon ta hanyar wayar da kan mutane a duniya.
Taken taron na bana shine ‘Samar da kula ga masu fama da ciwon’.
Mohammed ya ce kashi 90% daga cikin mutum miliyan 11.2 din dake fama da ciwon na fama da nau’in ciwon ‘Type 2 diabetes’ wanda kan lalata wasu bangarorin jikin mutum.
Ya ce zuwa yanzu mutum miliyan 537 ne ke fama da ciwon a duniya.
Mohammed ya yi kira ga gwamnati da ta kara kason kudin harajin da ta saka wa kayan zaki daga kashi 10% zuwa kashi 20% domin mutane su san illar da kayan zaki ke yi wa kiwon lafiya sannan da hana mutane shan su.
Mohammed ya yi kira ga gwamnati da ta saka cututtuka irin su ciwon siga cikin tsarin inshorar lafiya domin taimakawa wa masu fama da ciwon.
Ciwon siga na kama mutum ne idan aka samu matsala da wasu daga cikin ababen da ke sarrafa abincin da ake ci.
Insulin na aiki ne a jiki wajen tace sinadarin ‘Carbonhydrate’ dake cikin abincin da muke ci don samar wa mutum kuzarin da yake bukata a jiki.
A dalilin rashin aikin ‘Insulin’ yadda ya kamata ne ya ke sa a kamu da ciwon siga.
UN ta ce domin rage yaduwar wannan cuta za ta yi amfani da watan Nuwambar kowace shekara domin wayar da kan mutane sanin illoli da hanyoyin guje wa kamuwa da cutar.
Discussion about this post