Ma’aikatan Majalisar Dinkin Duniya a Najeriya, a ranar 13 ga watan Nuwamba 2023, sun bi sahun takwarorinsu na dukkan tashoshin da ke aiki a duniya domin yin shiru na minti daya domin tunawa da ma’aikatan Majalisar Dinkin Duniya da suka rasa rayukansu a yakin da Isra’ila da Hamas ke ci gaba da yi a Gaza.
“Yana da matukar bakin ciki cewa muna tare da dukkan jami’an Majalisar Dinkin Duniya a duk fadin duniya a dukkan tashoshin da ke aiki don yin shiru na minti daya a yau Litinin, 13 ga watan Nuwamba, 2023 don girmama abokan aikinmu da aka kashe a Gaza.” Mukaddashin Mazaunin Majalisar Dinkin Duniya kuma mai kula da ayyukan jin kai a Nijeriya, kuma Wakilin Shirin Ci Gaba na Majalisar Dinkin Duniya, Mohamed Yahya, ya bayyana haka a wani takaitaccen taro da aka saukar da tutar Majalisar a zauren Majalisar Dinkin Duniya a Abuja.
“Kamar yadda kuke gani, an saukar da tutar Majalisar Dinkin Duniya zuwa rabin-girma a matsayin alamar girmamawa a wannan taro. “Ina so in nemi dukkan mu da mu yi shiru na tsawon minti daya yayin da muke girmama abokan aikinmu da suka mutu,” in ji shi.
Bugu da kari, ya bukaci duka ma’aikatan da su shiga cikin taron, yana mai jaddada muhimmancin girmama tunawa da wadanda suka sadaukar da kansu wajen yi wa bil’adama hidima.
Bisa ga ka’ida, an kuma yi shiru na minti daya daga ma’aikata 86 da ke halartar taron koli na Majalisar Dinkin Duniya a Najeriya da ke gudana a jihar Neja. Da misalin karfe 1:30 na rana, mahalarta taron sun tashi don yin shiru na minti daya don girmama abokan aikinsu da suka mutu a Gaza.
Bayan shirun minti dayan ne, Yahaya ya kammala saƙon nasa da fatan alheri: “Allah ya sa sun huta.”
Discussion about this post