Gargaɗi, ragargaza da fatattakar da Shugaba Bola Tinubu ya yi wa ɗan sa Seyi da wasu hadiman sa cewa kada wanda ya ƙara shige taron Majalisar Zartaswa, ya janyo ra’ayoyin jama’a daban-daban a soshiyal midiya, kuma an jama’a an ƙara sa-ido sosai kan iyalan Shugaban Ƙasa.
A ranar Litinin ce dai Shugaba Tinubu a wurin taron Majalisar Zartaswa ya nuna ɓacin rai yadda ya ga waɗanda ba a gayyata taron sun shiga ba, cikin su kuwa har da ɗan sa Seyi mai shekaru 37 a duniya.
“A taron makon da ya gabata na lura da wasu da ba a gayyata taron ba, sun riƙa shigowa, sannan su na sulalewa daga zauren Majalisar nan. Ciki na ga an nuno har da hoton ɗa na Seyi can a baya ya na zaune. To wannan ba zai ƙara yiwuwa ba,” inji Tinubu.
Daga nan ya lissafa sauran waɗanda za a riƙa bari su na shiga taron Majalisar Zartaswa, waɗanda ya ce sun haɗa da Hadiza Bala, Mashawarciyar Musamman a Tsare-tsaren tafiyar da Mulki; Bayo Onanuga, Mashawarcin Musamman a Fannin Yaɗa Labarai; Hakeem Muri-Okunolawanwanda shi ne Babban Sakataren Bola Tinubu da kuma Sakatare Damilotun Aderemi.
Waɗanda dokar ƙara ta amince su shiga taron dai sun haɗa da Shugaban Ƙasa wanda shi ne Shugaban Majalisar Zartaswa, Mataimakin Shugaban Ƙasa, wanda shi ne Mataimakin Shugaban Majalisar Zartaswa, Ministoci, Sakataren Gwamnatin Tarayya, Shugaban Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya da wasu manyan hadiman shugaban ƙasa.
A yanzu dai a ranar Litinin ake yin taron, maimakon ranar Laraba, kamar yadda gwamnatocin baya suka riƙa yi.
Ra’ayoyin ‘Yan Najeriya:
‘Yan Najeriya da dama sun yaba wa Shugaba Tinubu ganin yadda ya fito fili ya gargaɗi ɗan sa cewa kada ya ƙara shiga Majalisar Zartaswa.
Wani mai suna Charles ya shiga shafin sa na X wato Tiwita, inda ya ce “Seyi Tinubu na fama da giggiwa, kan sa na hayaƙi wai shi ɗan Shugaban Ƙasa. Amma na ji daɗin yadda Tinubu ya taka masa burki.”
Wani mai suna Ayo Akin ya bayyana cewa yanzu fa ba irin mulkin da ya gabata ba ne. Wannan shugaban ya nuna shi da gaske ya ke yi.”
Jama’a da dama sun yi ta tofa albarkacin bakin su, tare da nuna cewa hakan da Shugaba Tinubu ya yi daidai ne.
Idan za a tuna, cikin Oktoba Seyi ya je kallon wasan folo Kano a cikin jirgin Shugaban Ƙasa. Wannan lamari kuwa bai yi wa ‘yan Najeriya daɗi ba.
Sai dai kuma wasu sun riƙa cewa Shugaban Ma’aikata, Femi Gbajabiamila ne ya bada umarnin a kai Seyi Kano a cikin jirgin, ba tare da sanin Tinubu ba.
Kada a manta, lokacin mulkin Buhari an samu sakaci a cikin Fadar Shugaban Ƙasa, har iyalan ɗan uwan sa Mamman Daura su ka yi hayaniya da iyalan Shugaban Ƙasa, kuma rikicin ya watsu a soshiyal midiya.
Discussion about this post