Watanni takwas bayan Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta gudanar da zaɓen da ya fi sauran zaɓuka haifar da ce-ce-ku-ce a Najeriya, a watannin Fabrairu da Maris, INEC ta sake fuskantar caccaka da ragargaza dalilin irin jagwalgwalo da bahallatsar da ake ganin ta yi wajen gudanar da zaɓukan gwamnoni uku a jihohin Bayelsa, Imo da Kogi a ranar 11 ga Nuwamba.
Rahotannin da kafafen yaɗa labarai da ƙungiyoyin sa-ido suka fitar bayan kammala zaɓen sun nuna kamanceceniyar irin jagwalgwalon aka yi a zaɓen Fabrairu da Maris a wannan zaɓe na Nuwamba, a jihohin uku.
A yanzu jama’a sun ƙara fitar da rai daga tunanin samun sahihin zaɓe daga INEC, kuma sun daina gaskata hukumar kwata-kwata.
An yi tunanin irin yadda aka narka maƙudan kuɗaɗe wajen girke jami’an ‘yan sanda 40,000 a Kogi, 27,000 a Bayelsa da kwamishinonin INEC 84 a Imo, to za a samu sauƙin maguɗi da harankazamar hauma-haumar zaɓe a jihohin uku. Amma sai hakan bai samu ba.
Masu lura da al’amurran zaɓe da dama sun haƙƙaƙe cewa har yau a ƙasar nan sai an ɗauki shekaru da dama nan gaba kafin a fara tunanin samun sahihin zaɓe daga INEC.
Masu adawa da nasarar da Gwamnonin Imo da Bayelsa su ka samu a tazarcen da suka yi, da waɗanda ke adawa da nasarar da Usman Ododo ya samu a Kogi, su na kururuwar an yi masu maguɗi, tare da nuna ƙarara irin yadda aka riƙa danne haƙƙin abin da talakawa suka zaɓa.
Ɗakunan Tattara Bayanan Sakamakon Zaɓe na Ƙungiyoyin Kare Dimokraɗiyya sun tabbatar da mutuwar irin harankazamar da aka yi da sunan zaɓe a jihohin uku. Kuma hakan ya nuna cewa INEC ta rasa wata dama a wannan karon wadda za ta wanke kan ta daga zargin da jama’a ke yi mata, tare da cusa masu amincewa da hukumar a zuciyar su.
Su ma jam’iyyun siyasa sun ƙara tabbatar da zargin da mutane ke yi masu, cewa ba su iya cin zaɓe sai da ƙarfa-ƙarfa, harambe, rikici, maguɗi da tsiya ko da tsinin-tsiya.
Hukuncin da jama’a ke yi wa INEC da jam’iyyu kan zaɓen shi ne, “bai cika sharuɗɗan zama sahihin zaɓe ba.” Hakan kuwa ya sa darajar INEC da zaɓen sun zube ƙasa warwas.
Idan har INEC a ƙarƙashin jagorancin Mahmood Yakubu ba ta iya kallon madubi ta ga irin yadda ƙyasfi ya lalata mata fuska a zaɓukan baya, a zaɓen gwamnonin nan uku ya kamata ta yi hakan. Tabbas munin tabon da ke jikin fuskar INEC, ya disashe duk wani annurin da ke kan fuskar.
Dama kuma shi wannan zaɓe na jihohi uku da aka yi cikin Nuwamba, ya samo asali ne tun daga wata karimtsa da rimatson zaɓe da aka yi cikin 2007, inda tun daga nan ba a sake yin zaɓen gwamna a jihohin tare da sauran jihohin Najeriya a lokaci ɗaya ba.
A zaɓen nan na Nuwamba, an ga yadda aka rubuta sakamakon zaɓen wata ƙaramar hukuma tun ma kafin a fara zaɓe aka ga takardun sakamakon na yawo. Har yanzu INEC sai kame-kame ta ke yi.
An ga yadda INEC ta yarda ta tafka kurakurai a wasu rumfunan zaɓe 59 da ta ce a sake zaɓe a ranar 18 Ga Nuwamba.
An ga yadda aka riƙa sayen masu jefa ƙuri’a daga Naira 1,000 zuwa Naira 30,000, a fili ba a ɓoye ba.
Ga kuma fizgen akwati, hargitsa ƙuri’u, tashe-tashen hankula, firgita masu zaɓe, yi masu barazana, fatattakar masu zaɓe da kashe-kashe, baddala sakamakon zaɓe da cumuimuye takardun sakamakon zaɓe.
Mun ga yadda aka riƙa kauce wa bin tsarin BVAS, alhali ƙasar nan kuma ko kunya mahukunta ba su ji, su na ta yage baki wai dimokraɗiyya na tasiri a Najeriya.
Ya kamata idan ido da kunya, to waɗanda aka ayyana sun yi nasara a irin wannan zaɓen, su daina fitowa su na tsallen sun yi nasarar ƙarya.
Ƙungiyoyin sa-ido a zaɓe masu daraja irin su CDD da Yiaga Africa da wasu da dama sun kalli shirme da rashin adalcin da ya faru a wurare da dama lokutan zaɓe, wanda hakan ya sa suka fito suka faɗa wa INEC gaskiya cewa “ta sake bibiya da bin diddigin yadda aka gudanar da zaɓen Kogi da Imo, domin ta tantance wuraren da aka tafka maguɗi, ta maida wa masu haƙƙin ƙuri’u haƙƙin su.”
Kuma sun yi ƙoƙarin cewa INEC ta ƙi tsayawa tantance yadda aka yi aringizon ƙuri’u a lokacin zaɓukan a wasu wurare.
Hauka ne sosai a ce yawan ƙuri’un da aka jefa a lokacin zaɓe sun haura yawan ƙuri’un da aka tantance, kuma INEC ta rufe ido karɓi sakamakon zaɓen. Hakan ya faru a Imo a 2019, kuma ya sake faruwa a Imo, a zaɓen Nuwamba, 2023.
Ku dubi yadda a Jihar Kogi INEC ta kauda ido daga kukan da ɗan takarar PDP, Dino Melaye ya yi, inda aka kama ma’aikacin INEC ɗan NYSC da Naira miliyan 1. Shiru ka ke yi, wai malaman INEC sun ci shirwa.
An yi zargin cewa jami’an INEC sun sayar da zaɓen ƙananan hukumomin Adavi, Ajaokuta, Ogiri/Magongo, Okehi da Okene a Kogi la’ada waje. Kuma tilas INEC ta yi alƙawarin cewa za ta duba lamarin. Doka ta bai wa INEC kwanaki bakwai ta tantance zargin cewa sai ƙuri’un da aka tantance ne kaɗai za a sanar. Amma har yau shiru ka ke ji.
Ta yaya aka yi har INEC ta bari aka jefa ƙuri’u 84,000 da ta soke, waɗanda aka jefa wa Timipre Sylva na APC daga yankin Nembe da ƙananan hukumomin kudancin Ijaw a jihar Bayelsa? Akwai shari’a a kotu nan gaba kenan.
Irin yadda zaɓe ya lalace a Najeriya sai ƙara muni abin ke yi, saboda ba a hukunta masu laifin dagula shi. Su kuma wasu alƙalai sai bada kai suke yi borin wasu ‘yan siyasa na hawa.
Muddin ana so a fara gyara wannan shaiɗancin da ake yi lokutan zaɓe, to a yanzu ne Shugaba Bola Tinubu zai fara da gaggawa, idan har da haske yake yi. Kuma farkon abin da zai fara yi, shi ne a soke naɗin kwamishinonin INEC huɗu da ya yi wa ‘yan APC kwanan nan, dokin naɗin na su ya karya dokar kundin tsarin mulkin Najeriya.
Idan ba a yi haka ba kuwa, to ko yanzu, ko ba-jima, ko ba-daɗe, wannan dimokraɗiyyar durƙushewa za ta yi, domin nauyin shrime, harigido, zalinci da rashin adalcin da ke cikin ta sun kusa rugurguza ƙafafun da ke ɗauke da ita kan ta dimokuraɗiyyar.
Discussion about this post