Daga cikin naɗe-naɗen muƙamai da Shugaba Bola Tinubu ya yi ga mutanen da ake ganin kwata-kwata ba su cancanta ba, wanda ya fi haɗari ƙiri-ƙiri a fili shi ne naɗin da ya yi Kwamishinonin Hukumar Zaɓe ta Ƙasa ga wasu masu alaƙa da jam’iyyar APC mai mulki.
Baya ga cewa naɗin haramtacce ne, sannan kuma barazana ce da kuma hatsarin gaske ga ɗorewar dimokraɗiyya a Najeriya. Kuma rashin adalci ne, rashin ya-kamata ne, kuma rashin mutunci ne ga ƙimar ‘yan Najeriya da tsarin zaɓe, domin Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na 1999 ya haramta naɗa wanda ke da alaƙa ta kusa ko ta nesa da wata jam’iyya a muƙamin, ballanata kuma mamba na jam’iyya wanda har muƙamai ya riƙe a ƙarƙashin mulkin APC.
Babban abin mamaki shi ne yadda Majalisar Dattawa ta tantance Etekamba Umoten daga Akwa Ibom da Isah Ehineakne daga Jihar Edo, duk kuwa da cewa PREMIUM TIMES ta bankaɗo alaƙar su da APC, tare da nuna haɗarin da ke tattare da dimokraɗiyyar ƙasar nan idan har aka naɗa su kwamishinonin INEC.
Mutane ne da aka tabbatar da cewa ko dai makusantan Shugaba Tinubu ne, ko kuma mambobin APC ne.
Haka kuma akwai wasu biyu wato Bunmi Omoseyindemi daga Jihar Legas da kuma Anugbum Onuoha daga Jihar Ribas, waɗanda su ma majiɓinta APC ne idan aka dubi naɗe-naɗen da aka taɓa yi masu baya-bayan nan.
‘Yan Majalisar Dattawa sun ga irin ƙorafe-ƙorafen da aka riƙa yi kan mutanen nan, kuma sun san haramcin naɗa su, amma kuma ƙiri-ƙiri suka tantance su.
Maganar da ake yi yanzu ita ce, ta yaya za a yi tunanin cewa INEC zaman kan ta ta ke yi, ba zaman gwamnatin da ta naɗa jami’an ta ta ke yi ba? Ta yaya za a amince da sahihancin zaɓen da INEC za ta riƙa gudanarwa.
PREMIUM TIMES ta bayyana irin kusancin da Umoren ke da shi ga Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio. Haka shi ma Isah na Jihar Edo jaridar ta tabbatar da ɗan a-mutum Bola Tinubu ne, ya ma yi masa kamfen wurjanjan kafin zaɓen shugaban ƙasa.
Haka Bunmi Omoseyindemi daga Legas, yaron Tinubu ne. Onuoha daga Jihar Ribas yaron tsohon Gwamnan Ribas, Nyesom Wike ne, wanda a yanzu Wike shi ne Ministan Babban Birnin Tarayya, FCT, Abuja. Dukkan waɗannan ba’arin mutane huɗu da Tinubu ya naɗa Kwamishinonin Zaɓe haramtattu ne. PREMIUM TIMES ta faɗi haramcin su, kamar yadda shi ma Babban Lauya Femi Falana da sauran lauyoyi da ƙungiyoyi su ka bayyana tare da yin gargaɗi.
Sannan abin ɗaure kai da kuma takaici shi ne yadda aka naɗa Umoren Kwanishinan Zaɓe daga Ribas, alhali wa’adin Udo Tom ɗan Jihar Ribas saura watanni uku ya cika, domin sai cikin Janairu, 2024 wa’adin sa zai cika.
Naɗe-naɗen Kwamishinonin Zaɓe da Tinubu ya yi da kuma yadda Majalisar Dattawa ta tantance su, ya nuna ƙarara cewa shiri ne ake ƙullawa domin haifar da barazana ga sahihancin zaɓukan da za a gudanar nan gaba.
A bayan an yi irin wannan naɗin lokacin mulkin tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari cikin 2019, amma da aka farga daga baya, sai aka janye naɗin, wanda aka yi wa Olalekan Raheem matsayin Kwamishinan Zaɓe daga Jihar Osun, saboda an gano cewa ɗan APC ne.
Abin mamaki, Majalisar Dattawa ta hana naɗa Raheem a zamanin Buhari, amma kuma yanzu a zamanin Tinubu ta amince da naɗin har mutum huɗu ‘yan APC.
PREMIUM TIMES na kira ga Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya gaggauta soke naɗin waɗannan Kwamishinonin Zaɓe huɗu. Idan bai yi hakan ba kuwa, to ta tabbata cewa za a riƙa yi masa kallon shugaban da ya hau mulki ɗauke da makara da likkafanin turbuɗa dimokraɗiyyar Najeriya cikin kabari, bayan ya yi mata munmunan kisan-gilla.
Discussion about this post