Jami’an rundunar ‘yan sandan Kaduna sun kama wani matashi mai suna David Felix mai shekaru 20 a kauyen Madakiya dake Zangon Kataf bisa zargin aikata laifin kisa.
Ana zargin Felix da kashe mahaifinsa.
Felix ya faɗi a bainar manyan gida da dattawa cewa ya kashe mahaifinsa ne a dalilin mafarkin da ya yi inda ya ga mahaifin ya rikida ya zama tantabara da kan mutum ya bishi da guda yana neman ya kashe shi.
Wani mazaunin kauyen ya bayyana cewa Felix ya faɗi musu cewa a kullum dare sai ya yi mafarki da mahaifinsa.
Bayan ya shiga hannun ƴan sanda Felix ya ce ya maka wa mahaifinsa tabarya yayin da yake barci inda daga nan bai sake motsi ba ballantana ya farka daga barcin.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Mansir Hassan ya ce za su kai Felix kotu da idan sun kammala gudanar da bincike.
Discussion about this post