Kungiyar SERAP, ta BudgIT da kuma wasu ɗaiɗaikun ‘yan Najeriya 34, sun maka Shugaba Bola Tinubu a Babbar Kotun Tarayya ta Abuja, saboda “naɗa aƙalla mambobin jam’iyyar APC su huɗu a matsayin kwamishinonin Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC).”
Majalisar Dattawa dai ce ta rufe ido tare da toshe kunnuwan ta daga ƙorafe-ƙorafen ‘yan adawa da ƙungiyoyi da sauran ‘yan Najeriya, cewa naɗin na su haramtacce ne.
Cikin waɗanda aka naɗa ɗin har da wasu daga Jihar Akwa, Edo, Lagos da Jihar Ribas.
A cikin kwafen ƙarar da su SERAP suka shigar mai lamba FHC/L/CS/2353/2023, a ranar Juma’a, a Babbar Kotun Tarayya, Legas, masu ƙarar na neman kotu ta jingine naɗin kwamishinonin huɗu, a soke tantancewar da Majalisar Dattawa ta yi masu, saboda ta saɓa dokar Najeriya, sannan kuma ta haramta naɗin kwata-kwata.”
Haka kuma sun nemi kotu ta tilasta tare da bai wa Shugaba Bola Tinubu da Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio umarnin gaggauta cire su daga kwamishinonin INEC, domin naɗin su ya karya Sashe na 157 na Kundin Dokokin Najeriya, na 1999 wanda aka yi wa kwaskwarima.”
Kwanan baya sai da wani lauya ya fito ya ya ce Sanata Akpabio ya raina hankalin ‘yan Najeriya, kamar yadda ita ma jam’iyyar PDP ta ƙi yarda da naɗin.
Lauya ɗan rajin kare haƙƙin jama’a shi da kwanciyar PDP sun ƙi amincewa da naɗin da Shugaba Bola Tinubu ya yi wa makusancin Shugaban Majalisar Dattawa Godswill Akpabio, a matsayin Kwamishinan Zaɓe.
Lauya Inibehe Effiong ya ce ba zai yiwu Akpabio ya raina wayon ‘yan Najeriya ba, har ya amince a naɗa mutumin da Etwkamba Umoren wanda ɗan APC muƙamin Kwamishinan Zaɓe daga Jihar Akwa Ibom.
Naɗin da Shugaba Tinubu ya yi wa Umoren dai haramtacce ne, bisa dokar Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na 1999.
Amma duk da rashin amincewa da ƙorafe-ƙorafen jama’a, Majalisar Dattawa a ƙarƙashin jagorancin Akpabio ta amince da naɗin sa.
Umoren dai ɗan asalin ƙaramar hukumar Akpabio ne, wato Ƙaramar Hukumar Essien Udim.
Kuma shi ne Babban Sakatare a Gidan Gwamnati, lokacin mulkin Akpabio da ya na gwamnan Akwa Ibom.
Akpabio ya sa gwamnan da ya gaje shi, Udom Emmanuel ya naɗa Umoren Sakataren Gwamnatin Akwa Ibom.
Amma an cire shi a Janairun 2018, bayan an ɓata tsakanin Akpabio da Emmanual.
Lokacin da Akpabio ya zama Ministan Harkokin Neja Delta cikin 2019, ya naɗa Umoren a matsayin Shugaban Ma’aikata.
Tuni dai naɗin Umoren yanzu a matsayin Kwamishinan Zaɓe ya fusata Lauya Effiong, wanda ya ce abin kunya ne, rainin hankali ne ga ‘yan Najeriya.
Ya ce hakan ya nuna kamar babu wani mutum nagari kenan da za a naɗa daga Akwa Ibom sai Umoren.
Effiong ya ce wannan abu da Akpabio ya yi, ba wannan karon ne farau ba, kuma matsalar da shi kenan, koda yaushe a dungu yake, ba ya tafiyar da al’amuran kai-tsaye.
‘An Naɗa Umoren Kwamishinan Zaɓe Don Ya Shirya Maguɗi Da Tuggu A Zaɓuka’ -PDP:
Jam’iyyar PDP ta bayyana cewa ba ta amince da naɗin da Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya Yi wa Kwamishinan Zaɓe Umoren da Akwa Ibom ba.
PDP ta ce an naɗa ɗan APC Kwamishinan Zaɓe ne da gangan domin ya taimaka wa APC wajen yin maguɗi, bada haɗin kai wajen damalmala bayanan INEC, hargitsa tsare-tsaren bayanan zaɓe cikin har da na rajistar masu zaɓe da baddala sakamakon zaɓe a jihar Akwa Ibom.”
Kakakin PDP na Ƙasa, Debo Ologunagba ne ya bayyana haka a ranar Alhamis, yayin ganawa da manema labarai.
Ruguguwar Naɗin Kwamishina A Cikin Wa’adin Wani Kwamishina:
PREMIUM TIMES ta kuma buga labarin cewa Tinubu ya kwafsa, na ya naɗa Kwamishinan Zaɓe daga Akwa Ibom, alhali wa’adin wanda ke kai bai ƙare ba.
Shugaba Bola Tinubu ya tafka shirme, yayin da ya kwafsa wajen naɗa Etekamba Umoten daga Jihar Akwa Ibom, matsayin Kwamishinan Zaɓe (REC), yayin da wa’adin wanda ke kai, bai ƙare ba tukunna.
Binciken da PREMIUM TIMES ta gudanar ya tabbatar da cewa Monday Udo-Tom, ɗan asalin Jihar Akwa Ibom, wanda a yanzu shi ne Kwamishinan Zaɓen Jihar Bayelsa, wa’adin sa bai ƙare ba, har sai cikin Janairu, 2024 tukunna.
Kenan idan a yanzu aka rantsar da Umoren matsayin sabon Kwamishinan daga Jihar Akwa Ibom, zai kasance jihar na da kwamishinoni biyu kenan.
Wannan kuwa ƙarara ya nuna cewa Tinubu ya karya dokar ƙasa, kamar yadda ya karya, inda ya naɗa ‘yan APC biyu a matsayin Kwamishinonin Zaɓe.
Dama kuma a makon da ya gabata ne Tinubu ya yi naɗin yayin da a cikin wannan makon kuma Majalisar Dattawa ta amince da waɗanda ke da alaƙa da jam’iyyar siyasa, duk kuwa da cewa ƙungiyoyi daban-daban sun nuna rashin amincewa kan hakan.
Sannan kuma Umoren ɗin nan ya na ɗaya daga cikin waɗanda doka ta haramta a naɗa, saboda ya na da alaƙa da jam’iyyar APC.
Haka nan kuma Umoren ya na da kusancin siyasa da Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, domin ya taɓa zama Shugaban Ma’aikatan Gidan Gwamnatin Akwa Ibom, lokacin da Akpabio ke gwamna.
Na biyu ɗin mai alaƙa da APC shi ne Isa daga Jihar Edo, wanda aka haƙƙaƙe cewa shi har ma katin shaidar rajistar ɗan APC gare shi.
Discussion about this post