Hukumar Kididdiga ta Kasa (NBS) ta sanar a ranar Laraba cewa, hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya ya karu zuwa kashi 27.33 a watan Oktoba daga kashi 26.72 cikin dari a watan da ya gabata.
Ofishin kididdiga ya ce adadin hauhawar farashin kayayyaki a watan Oktoba na shekarar 2023 ya nuna karuwar kashi 0.61 cikin 100 idan aka kwatanta da hauhawar farashin kayayyaki a watan Satumbar 2023.
Hukumar ta NBS ta ce idan za ayi dubi da hauhawar na shekara-shekara, hauhawar farashin kayayyaki ya kan tsaya ne a daidai kashi 6.24 bisa 100, yayin da idan aka kwatanta da na watan Oktoban 2022, wanda ya kai kashi 21.09 cikin 100.
Hakan na nuna cewa an samu hauhauwar farashin kayayyaki da ya yi ƙololuwa a Oktobar 2023, idan a ka kwatanta da Oktobar 2022.
A wannan shekara farashin kayan abinci ya yi tashin gwauron zabi a fadin Najeriya. Lamarin dai ya tabarbare ne sakamakon tasirin manufofin gwamnati kamar cire tallafin man fetur da dai sauransu.
A Najeriya yanzu, ana cikin matsanancin matsi na rayuwa a dalilin hauhawar farashin kayan abinci da na masarufi.
Discussion about this post