A ranar Talata ce Manyan Shugabannin Ɓangarorin Tsaron Ƙasa, ciki har da Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, suka bayyana a gaban Majalisar Tarayya, domin zama na musamman kan yadda za a daƙile matsalar tsaron da ke sake kunno kai, musamman ta Boko Haram da ke sake dannowa yanzu.
Waɗanda suka halarci gayyatar da majalisar ta yi masu, sun haɗa da Babban Hafsan Tsaron Ƙasa, Christopher Musa; Hafsan Hafsoshin Askarawan Najeriya, Taoreed Lagbaja da Hafsan Hafsoshin Sojojin Ruwa, Emmanuel Ogala.
Sauran sun haɗa da Hafsan Hafsoshin Sojojin Sama, Hassan Abubak da kuma Sufeto Janar na ‘Yan Sandan Najeriya, Kayode Egbetokun.
Da ya ke jawabi, Babban Hafsan Hafsoshin Tsaron Najeriya, Musa, ya ɗora laifin sake fantsamar ta’addancin Boko Haram kan alƙalan Najeriya.
Ya ce su ke da laifi, domin idan sojoji sun kama Boko Haram a hannu, sai alƙalai su sake su idan an je kotu.
“Na yi aiki a Arewa maso Gabas, an kama gaggan ‘yan Boko Haram da dama. Mun tsare su tsawon shekaru biyar zuwa shida. To mu kuma sojoji sai dai mu kama kawai, amma ba mu iya gurfanar da su kotu.
“An samu da dama a cikin su da laifi, amma ba a gurfanar da su kotu ba.
“Tsare su da muke yi na tsawon lokaci, sai a riƙa zargin mu da take haƙƙin ɗan Adam.
“Sannan kuma wata matsalar ita ce alƙalan kotuna, waɗanda sai mun yi iyakar ƙoƙarin mu mun kama ‘yan Boko Haram, sai su sake su idan mun damƙa su.
“Kafin ka shiga mota bayan ka damƙa su, sai alƙali ya sake su, ya bada su beli.
“To kun ga kai ka sayar da ranka wajen kama su; yayin da aka sake su, sai su je su na sanar da mutane jami’in tsaron da ya kama su. Ka ga iyalin kai da ka kamo ɗan Boko Haram sun shiga tasku kenan. Kullum su na kwana cikin barazana da jimami,” cewar Musa.
Ya ce yanzu abin na nema ya kai har jami’an tsaro ba su ma so su kama ɗan Boko Haram.
“Irin haka mu ke fama a yankin Kudu maso Kudu, inda jirgin ruwan da muka kama shekaru goma baya, sai ga shi an sake shi, an sake raɗa masa wani suna daban, aka sake masa kalar wani fenti daban, aka sake maido shi ruwa ya na zirga-zirgar sa.
“Don haka akwai buƙatar a duba wannan lamarin sosai.
“Tilas ya zamanto akwai kotunan musamman masu hukunta irin waɗannan masu laifin. Dalili kenan da mun kama jirgin ruwan da ake sata ko fashi da shi, kawai sai dai mu gaggauta tarwatsa shi. Saboda idan ya daɗe to akwai matsalar za’a iya sakin sa idan an je kotu.”
Ya ƙara da cewa a kan ma matsa masu lamba su saki jiragen ruwan da suka kama.
Ya ce a yanzu akwai ‘yan Boko Haram 140,000 da suka yi saranda.
Discussion about this post