Kungiyar masana ilimin haɗa magunguna na Najeriya PSN ta bayyana cewa kwararrun sama da 7,000 ne suka fice daga kasar nan zuwa kasashen waje a cikin shekaru biyu da suka wuce.
Shugaban kungiyar Cyril Usifoh ya sanar da haka ranar Talata a taron kungiyar ta da aka yi a jihar Gombe.
Usifoh da yake ganawa da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN ya ce masanan na ficewa daga kasar nan zuwa kasashen wajen domin neman aikin da ya fi wanda suke yi a Najeriya.
Ficewar jami’an lafiya na daga cikin matsalolin dake kawo cikas a fannin lafiyar kasar nan da ya kamata gwamnati ta maida hankali a akai.
A jawabinsa a wurin taron, Shugaban kungiyar ya ce wannan karon su za su tattauna hanyoyin inganta fannin kiwon lafiya da kuma tattauna yadda za a shawo kan matsalolin da fannin ke fama da su.
Discussion about this post