Fitaccen ɗan fim ɗin Nollywood Hanks Anuko, ya yi kururuwar neman agajin neman tallafin kuɗaɗe daga wajen masoyan sa.
A wata sanarwar da ya yi a shafin sa na Instagram, a ranar Alhamis, Anuko mai shekaru 62 ya ce talauci ya yi masa katutu a halin yanzu, don haka ya na neman tallafi, kuma ya na godiya ga ɗimbin masoyan sa, tun ma kafin su kai ga fara tallafawar.
Wannan neman agajin gaggawa da Anuko ya yi, ya fito ne kwana ɗaya bayan an gan shi ya na watangaririya kan titi, a garin Asaba, Jihar Delta, wato jihar sa ta haihuwa.
Cikin shekarar da ta gabata ne Anuko ya tattauna da PREMIUM TIMES, inda har ya ce zai fito takarar shugabancin Najeriya.
Hanks Anuko dai tauraruwar sa ta fara haske a finafinai tun fitowar sa cikin ‘Broad Daylight’, a 2001 da kuma ‘Formidable Force’ cikin 2002.
A shekarun nan sunan Hanks na ta kewaya soshiyal midiya, saboda raɗe-raɗin ciwon taɓuwar ƙwaƙwalwa da ake zargin ya same shi, musamman ganin yadda ya ke yawo da kaya hargitsai, jikin sa kuma babu kimtsi, sannan ya kan yi ‘yan dambatu.
Anuko a cikin roƙon da ya yi, ya gode wa Gwamnan Delta Sheriff Oborevwori, sannan kuma ya nemi taimako daga gare shi.
A shafin sa na Tiwita, ɗan fim ɗin har adadin sauran kuɗin da ke asusun ajiyar sa na banki ya buga, wanda tatas ya ke.
Ya ce duk abin da ya samu zai yi matuƙar godiya, domin maganar gaskiya, ya na fama da matsanancin talauci.
Ya taɓa riƙe muƙamin Mashawarcin Musamman kan Buɗe Ido da Nishaɗi a Jihar Delta. Kuma cikin 2014 ya koma Ghana da zama, daga baya ya dawo Najeriya.
Discussion about this post