Kungiyoyin kwadago na NLC da TUC sun yaba wa gwamnatin jihar Kaduna da ta biya Naira biliyan 3.1 kuɗin fanshon ma’aikatan jihar da suka yi ritaya da wadanda suka rasu.
A wasika dake dauke da sa hannun Shugaban kungiyar NLC reshen Kaduna, Ayuba Suleiman ya mika godiyarsa ga gwamnan Uba Sani da ya biya wadannan kudade musamman a wannan lokaci da ake fama raɗaɗin cire tallafin mai a kasa baki ɗaya.
Suleiman ya ce kudaden da gwamnati ta biya zai taimaka wajen rage wahalhalun da ma’aikatan da suka yi ritaya da iyalan wadanda suka mutu ke fama da su a musamman wannan lokaci.
Tun bayan haka mutanen jihar ke yi wa gwamna Sani ambaliyar yabo da godiya bisa wannan kokari da ya yi na tausaya wa ƴan fanshon jihar.
Discussion about this post