Hukumar Lafiya ta Majalisar Ɗinkin Duniya (WHO), ta tabbatar da kisan da sojojin Isra’ila su ka yi wa wata ma’aikaciyar hukumar.
Haka nan kuma an kashe ɗan ta mai watanni shida da haihuwa, mijin ta da wasu ‘yan’uwan ta maza su biyu.
Shugaban WHO na Duniya, Adhanom Tedros Ghebreyesus ne ya bayyana haka da kan sa, cikin wata sanarwar da ya fitar a ranar Talata, a shafin sa na Tiwita, wanda a yanzu ake kira X.
An tarwatsa gidan iyayen ma’aikaciyar da bam, wanda ke kudancin gaɓar ruwan Zirin Gaza.
A can ne ma’aikaciyar ta gudu ta ɓoye yayin da yaƙi ya yi muni a Arewacin Gaza inda ta ke aiki.
“Ban san irin kalaman da zan yi amfani da su domin nuna jimamin mu ba.” Haka Tedros ya bayyana a shafin sa na Tiwita.
Kisan ma’aikaciyar mai shekaru 29 ya girgiza Hukumar Lafiya ta Majalisar Ɗinkin, kusan za a iya cewa shi ne kisa na farko da aka yi wa wani ma’aikacin hukumar, tun bayan fara yaƙin farmakin da Isra’ila ke kaiwa a Zirin Gaza.
Majalisar Ɗinkin Duniya (UN) dai rasa ma’aikata 108 da ke aiki a ƙarƙashin UNRWA, wato Cibiyar Kula da Falasɗinawa ‘Yan Gudun Hijira.
Sannan kuma an ruguza gine-ginen UN ɗin har 67, waɗanda 17 daga cikin su hari ne na kai-tsaye, ba tsautsayi ba ne.
Haka dai Kwamishina Janar na UNRWA, Phillippe Lazzarini ya bayyana.
Discussion about this post