Ministan Harkokin Kuɗaɗe kuma Ministan Kula da Tattalin Arziki, Wale Edun, ya ce Najeriya ba za ta iya dogaro da ciwo bashi domin ayyukan raya ƙasa a kasafin 2024 ba.
Edun ya bayyana haka ranar Alhamis, lokacin da ya bayyana a gaban Kwamitin Majalisar Dattawa da na Tarayya kan Kashe Kuɗaɗe da Tsare-tsaren Kuɗaɗe, a Abuja.
Ya ce hanya mafi alheri kuma mafi dacewa da Najeriya za ta iya bi ita ce a ƙara kashe kuɗaɗe kawai wajen gina ayyukan da za su samar wa ƙasa kuɗaɗen shiga.
“Bila gaskiyar magana, yanayin da ake ciki yanzu a duniya ko a nan cikin ƙasa, bai fa yiwuwa mu dogara da ramto kuɗaɗe domin ayyukan kasafin kuɗi.
“Dama kuma mun samu ɗimbin basussukan da muka gada, tuli guda. Muradin mu shi ne mu rage yawan ciwo basussuka tare da ƙoƙarin dakatar da wawakeken giɓi a cikin kasafin 2024.
“A taƙaice ina so ku sani, yanzu a manyan ƙasashe masu ƙarfin tattalin arziki a duniya, su na rige-rigen ƙoƙarin rage tashin gwauron zabin tsadar rayuwa da tsadar kayayyaki, domin tattalin arziki ya samu bai wa zuba jari karsashin bunƙasa.”
Shugaban Kwamitin, Sani Musa ya nuna fargabar sa cewa akasarin kirdado da kintacen kuɗaɗen shigar da Ma’aikatu da Hukumomin Gwamnatin Tarayya suka gabatar, bai kai adadin wanda ita Gwamnatin Tarayya ta yi a kasafin 2024 ba.
Bashin Da Ake Bin Najeriya:
Cikin Satumba, Ofishin Kula da Basussukan da Najeriya ta Ciwo (DMO) ya ce adadin bashin da ake bin ƙasar nan ya kai Naira tiriliyan 87.38.
Hakan na nufin an samu ƙarin har kashi 75.29 kenan a cikin 2023.
A ƙarshen Afrilu 2023 dai adadin bashin ya na Naira tiriliyan 49.85, amma zuwa Satumba ya samu ƙarin Naira tiriliyan 37.53.
DMO ya ce ƙarin ya faru ne saboda zunzurun Naira tiriliyan 23.71, waɗanda gwamnatin tarayya ta karɓo ramce daga hannun Babban Bankin Najeriya (CBN).
Discussion about this post