Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta bayyana cewa ta bankaɗo shirin tada zaune tsaye da wasu magoya bayan wata jam’iyyar ke shirin yi a jihar.
Bisa ga bayanan da kakakin rundunar Abdullahi Kiyawa ya yi ya ce magoya bayan na shirin gudanar da zanga-zanga domin nuna rashin jin daɗin su ga hukuncin da kotun koli ta yanke game da zaben gwamnan jihar.
Kiyawa ya ce rundunar ta dauki tsauraran matakan da domin daƙile wannan shiri da kuma tabbatar da doka da oda a jihar har.
“Rundunar ta gargaɗi mutanen jihar da su zauna cikin kwanciyar hankali, sannan duk wanda ke kokarin gudanar da zanga-zanga ya yi hakan tare da kiyaye doka.
Ya ce kwamishinan ƴan sanda, Usaini Gumel, ya yi kira ga mutane da su kwantar da hankalansu, su guji gudanar da duk wata haramtacciyar taro ko zanga-zanga da ka iya kawo tashin hankali a fadin jihar.
Gumel ya kuma ce rundunar tare da sauran rundunonin tsaro dake jihar sun saka ma’aikatan su a wurare da dama a jihar domin tabbatar da tsaro a jihar.
Discussion about this post