A ranar Talata ne majalisar dokokin jihar Kano ta karbi bukatar karin kasafin kudi na naira biliyan 24 daga gwamnan jihar, Abba Yusuf.
Bukatar ta ranar Talata ta zo ne watanni biyu bayan da majalisar ta amince da karin kasafin kudi na Naira biliyan 58. An amince da bukatar a ranar 9 ga Oktoba.
Karin kasafin na daya da na biyu a karkashin gwamna Yusuf a yanzu sun haura sama da Naira biliyan 82, watanni shida bayan hawansa mulki.
Tsohon Gwamna Abdullahi Ganduje, wanda shine Yusuf ya gada ya sanya hannu kan kasafin kudi na Naira biliyan 268 na shekarar 2023 kafin ya bar mulki a watan Mayu.
Dubi da karin kasafin Naira biliyan 82, kasafin shekarar 2023 na jihar yanzu ya kai Naira biliyan 350.
Gwamna Yusuf ya ce za a yi amfani da kuɗaɗen ne wajen cigaba da ayyukan raya kasa a faɗin jihar.
Discussion about this post