Kotun daukaka kara da ke Abuja ta soke zaben Gwamna Caleb Muftwang na Jihar Filato.
Alkalan kotun dukkan su uku waɗanda suka yanke hukuncin ranar Lahadi sun ce ba jam’iyyarsa ta PDP ba ce ta ɗauki nauyin Muftwang a takarar da ya yi na gwamna ba.
Alkalan sun ce korafin da ɗan takarar APC Nantawe Gonshew ya shigar a gaban kotu cewa Muftang bai cancanci zama ɗan takarar gwamna na PDP ba domin ɗauki ɗori ɗori aka yi ba a bi ƙa’ida ba.
Kotu ta ce kin bin umarnin Kotun Jos da ta yanke hukuncin cewa lallai PDP ta gudanar da sahihin zaɓen fidda ɗan takara a faɗin jihar a wancan lokacin ya saɓa wa dokar zaɓe.
A dalilin haka kotu ta yi watsi da hukuncin kotun sauraren kararrakin zaɓen gwamna da ta baiwa Muftwang na PDP nasara.
Kotun ta umarci hukumar zaɓe ta janye satifiket ɗin da ta ba Muftwang ta ba Nentwe na APC sabon Satifiket sannan a rantsar da shi gwamnan jihar cikin gaggawa.
Discussion about this post