A ranar Juma’a ne gwamnatin Faransa ta ce za ta mayar da dala miliyan 150 da tsohon shugaban Najeriya, Sani Abacha ya sace ya ajiye su a kasar Faransa wa Najeriya.
Da take zantawa da manema labarai a Abuja ranar Juma’a, ministar harkokin kasashen Turai da harkokin wajen Faransa, Catherine Colonna, yayin ziyarar kwana guda da ta yi a Najeriya, ta ce a matsayin amsa bukatar da ma’aikatar shari’ar Najeriya ta gabatar, da kuma yarjejeniya da gwamnatin Amurka. Faransa ta amince da mayar da kudaden da Abacha ya sace a matsayin tallafi don ayyukan raya kasa.
“Na kuma sanar da shugaban kasa Tinubu cewa Faransa za ta mayar wa Najeriya kadarorin da Janar Sani Abacha da iyalansa suka sace daga Najeriya, wadanda dankare a faransa tun shekarar 2021,” in ji ta.
Da aka tambayeta kan tsarin dawo da kudaden ya yi kama da tilasta Najeriya yadda zata kashe kudinta, ta ba da amsar cewa babu ruwan Faransa da yadda Najeriya za ta kashe kudin, tace ” Akwai yarjejeniya tsakanin gwamnatin Najeriya da Iyalan Abacha kan yadda za a kashe kudaden.
A kiyasin da aka yi Janar Abacha ya sace sama da Dala Biliyan 2 zuwa 3 a lokacin ya na mulkin Najeriya kuma duka kudaden sun fito ne daga cinikin danyen mai da Najeriya ta yi a zamanin sa.
Discussion about this post