Ƙungiyar Ma’aikatan Wutar Lantarki na Ƙasa, NIEE, sun umarci dukkan mambobin su na ƙasa baki ɗaya cewa su tsunduma yajin aiki, domin bin umarnin da NLC ta bayar na tafiya yajin aiki a ranar Talata ɗin nan.
Cikin wata sanarwa da NUEE ta fitar a ranar Talata da safe, wanda babban sakataren ƙungiyar mai suna Dominic Igwebike ya sa wa hannu, ta roƙi dukkan mambobin su a faɗin ƙasar nan cewa kowa ya shiga yajin aiki daga safiyar Talata.
Sai dai kuma ana ganin cewa wannan yajin aiki zai iya durƙusar da ƙasar nan, bisa dalilin cewa ma’aikatan lantarki su ma sun shiga yajin aikin.
NLC da TUC ne suka hada umarnin a fara yajin aikin, biyo bayan fushin da suka nuna lokacin da ‘yan sanda a Jihar Imo suka gwaggwabji Shugaban NLC na Ƙasa, Joe Ajaero, kuma su ka ƙi bayar da haƙuri.
Fadar Shugaban Ƙasa ta ce, ‘yajin aikin NLC da TUC haramtacce ce ne’.
Fadar Shugaban Ƙasa ta bayyana cewa babu wani dalilin da zai sa Ƙungiyoyin Ƙwadago na Ƙasa, wato NLC da TUC su tsunduma yajin aiki, domin bai kamata ba, kuma haramtacce ne.
Sanarwar da ta fito daga Mashawarcin Shugaban Ƙasa na Musamman a Yaɗa Labarai da Tsare-tsare, Bayo Onanuga, a ranar Litinin, ta ce tafiya yajin aikin kawai wata maƙarƙashiyar yi wa gwamnati zagon-ƙasa ce kawai.
Sanarwar Onanuga ta ce babu wani dalilin da zai sa ƙungiyar ƙwadago ta ƙaƙaba wa sama da mutum miliyan 200 wahala, saboda wani al’amari da ya shafi Shugaban NLC shi kaɗai.
Onanuga ya ce Gwamnatin Bola Tinubu ba ta goyon bayan jami’an tsaro su ci zarafin kowane ɗan Najeriya.
Ya ce to kuma bai kamata abin ya kai ga tafiya yajin aiki ba, tunda Sufeto Janar na ‘Yan Sandan Najeriya, ya kafa kwamitin bincike.
Discussion about this post