Takunkumin karya tattalin ko dakatarwar da Ƙungiyar Ƙasashen Afrika (AU) ke yi wa ƙasashen da suka kifar da gwamnatocin dimokraɗiyya tun daga 2019 ba shi da wani tasirin hana ci gaba da kifar da gwamnatoci daban-daban.
Duk da irin matakan da aka riƙa ɗauka, hakan bai hana ci gaba da kifar da gwamnatocin dimokraɗiyya a Afrika, musamman Afrika ta Yamma ba.
Tsakanin Yuni 2019 zuwa Agusta 2023, AU ta dakatar da halascin mambobin wasu gwamnatocin mulkin soja na wasu ƙasashe a ƙarƙashin ƙungiyar, irin su Sudan, Burkina Faso, Nijar, Mali, Gini da na kwanan nan a Afrika ta Tsakiya.
Ita ma ECOWAS ta bi sahun AU ta zartas da takunkumin a Mali, Gini, Burkina Faso da Nijar.
Tun daga 2003 zuwa yau, AU ta dakatar da dukkan ƙasashen da aka yi juyin mulki, in banda Chadi.
Sudan, Mali da Burkina Faso an sake samun juyin mulki duk da takunkumin da ƙasashen suka fuskanta a baya. Haka a Nijar, Chadi, Gini da Gabon.
Wasu dalilan da ke sa tskunku ba ya tasiri a ƙasashen da ake kifar da gwamnati a Afrika, sun haɗa da son kai wajen zaɓen ƙasar da za a ƙaƙaba wa takunkumi.
Sannan AU ba ta iya cewa komai a inda aka yi dodoridon ƙara wa’adin shugabannin ƙasashe bisa karya dokar ƙasa.
Mun ga haka a Cote d’Ivoire cikin 2016, Gini cikin 2020, Gabon cikin 2023, Ruwanda a 2023 sai kuma Afirka ta Tsakiya a cikin 2023.
Ƙasashe da dama har yau bayan juyin mulki sun ƙi maida gwamnati hannun farar hula, kamar Mali da ta ce za ta maida mulki ga dimokraɗiyya cikin Fabrairu 2024, amma kuma a yanzu ta ɗaga.
Sannan masu juyin mulki na amfani da irin taɓargazar da shugabannin mulkin dimokraɗiyya ke yi, su na samun goyon baya daga talakawan ƙasashen da aka yi juyin mulkin, kamar a ECOWAS, wanda aka yi a Mali cikin 2020, Gini a 2021, sai a Nijar cikin 2023.
Discussion about this post