Kungiyar ɗalibai ƴan asalin jihar Kano NAKSS dake karatu a Jami’ar gwamnatin tarayya dake Jigawa FUD ta yi ikirarin cewa dalibai ƴan asalin jihar sama da 4,000 ba su iya biyan kudin makaranta ba a dalilin karin kudin da jami’ar ta yi.
Wasu daga cikin daliban da suka gudanar da tattaki sun yi kira ga gwamnatin Kano da ta taimaka wajen biyan kudin makarantar su domin su samu damar rubuta jarabawa da za a fara mako mai zuwa.
Shugaban kungiyar ya bayyana wa PREMIUM TIMES cewa daga cikin dalibai yan asalin jihar Kano 7,000 dake karatu a jami’ar 3,000 ne kadai suka iya biyan kudin makarantar su.
Kakakin kungiyar Ibrahim Yunusa ya ce tun a watan Janairu bayan jami’ar ta yi karin kashi 200% na kudin makaranta iyaye da dalibai ke kokarin biyan kudin makarantar amma da dama basu iya biya ba har yanzu.
Jami’ar FUD ta kara kudin makaranta daga naira 30,000 da 40,000 zuwa 100,000.
Wa’adin kwanakin biyan kudin makarantar da jami’ar ta bada zai kare a mako mai zuwa.
Yunusa ya ce tun bayan karin da jami’ar ta yi kungiyar su take kokarin ganawa da gwamnatin Kano domin ganin an tallafa wa dalibai amma sai gwamnatin ta biya kudin makarantar daliban jami’ar BUK ta yi biris da nasu.
“Mun rubuta wa sabon gwamnan jihar Kano wasikar bayan da aka kammala zabe inda ya umarce mu mu gana da kwamishinan ilimi na jihar inda muka je wajen sa da kwafin wasikar gwamnan amma har yanzu shuru ka ke ji.
“Kwanaki shida kadai suka rage cikin wa’adin kwanakin biyan kudin makaranta da idan suka cika daliban da basu biya ba za su koma gida.
Zuwa lokacin da aka rubuta wannan labari kwamishinan ilimin jami’o’i Yusuf Kofar-mata bai ce komai ba domin bai amsa kira ko sakon tes din da aka aika wayarsa ba.
Discussion about this post