Tsohon shugaba gaban Kasa Goodluck Jonathan ya bayyana cewa da gwamnan jihar Douye Diri bai ci zaɓe ba da dole ya ɗauke mahaifiyarsa dake Bayelsa ya maida ta Abuja.
Jonathan wanda ya fito daga Otuoke a karamar hukumar Ogbia a jihar ya taba zama mataimakin gwamna sannan kuma gwamnan jihar Bayelsa mai arzikin man fetur a kudu maso kudancin Najeriya.
Jonathan ya yaba kokarin gwamna Diri na kawo ƙarshen matsalar tsaro da ake fama da shi a jihar, yana mai cewa ” Da Diri bi yi nasara a zaben gwamnan jihar ba da, dole ya ɗauke mahaifiyarsa cak, ya maida ta Abuja da zama.
A karshe ya yi kira ga mutanen jihar su mara wa gwamnan baya domin cigaban jihar baki ɗaya
” Zaɓe dai, an yi an gama, kuma mun tabbatar da nasarar da PDP ta samu a zaɓen, saboda haka yanzu lokaci ne da zamu dawo mu haɗa kai domin cigaban jihar mu baki ɗaya.”
Discussion about this post