Gwamnan Babban Bankin Najeriya, CBN, Olayemi Cardoso, ya umarci bankunan kasuwanci cewa su ƙara narka hannayen jari, domin a kai ga samun cimma gejin dala tiriliyan 1.
Gwamnan na CBN ya faɗi haka a ranar Juma’a, lokacin da ya ke jawabi a Taro na 58 na Cibiyar Masu Ruwa da Tsakin Bankuna na Najeriya, a Legas.
A cikin Oktoba ne dai Shugaba Bola Tinubu ya bayyana cewa tattalin arzikin Najeriya zai iya kai Dala Tiriliyan 1 nan da shekarar 2026, sannan ya dangana har Dala Tiriliyan 3 nan da shekaru 10.
Da ya ke jawabi a ranar Juma’a, Cardoso ya bayyana cewa bankunan Najeriya ba su da isassun jarin da zai iya kai Dala Tiriliyan 1 ko da nan gaba ne, sai fa idan an ɗauki matakin gaggawa.
Ya ce idan aka yi la’akari da kirdadon bunƙasar tattalin da ake yi, to abu ne mai muhimmancin gaske a bibiyi ƙarfin arzikin bankuna domin a samu damar faɗaɗawa da bunƙasa tattalin arziki.
“Batun ba wai na saisaita tattalin hada-hadar kuɗaɗe ba ne a yanzu. Domin mun ma bayyana cewa nazarin da muka yi ya nuna tsarin hada-hadar kuɗaɗe ya nuna akwai haske a cikin lungun da ake ciki.
“To amma dai akwai buƙatar mu tambayi kan mu da kan mu cewa, shin bankunan Najeriya su na da wadataccen karin da wannan tsari da ake a kai ke buƙata domin a kai gaci kuwa, har a samu zunzurutun Dala Miliyan 1, zuwa nan da wasu shekaru kaɗan? To amsa sai a nan ita ce “A’a!” Tilas sai mun ɗauki mataki tukunna.
“Saboda haka hanya ɗaya wadda za a iya cimma wannan muradin ita ce bankuna su ƙara danƙara jari a bankunan na su.”
Discussion about this post