Gogarman tabbatar da kowa ya samu ilimi musamman, ƴaƴan talakawa a Najeriya da ma kasashen waje, farfesa Adamu Gwarzo ya bayyana cewa burin sa shine ya ga akalla yara sama da miliyan ɗaya sun samu ilimi a faɗin kasar nan.
Burin farfesa Gwarzo shine ya tabbata Ilimi ya wanzu a ko’ina a faɗin ƙasar nan.
Da yake jawabi a lokacin da yake tabbatar da soma karatu a jami’ar Canada dake Abuja, wanda ɗaya ne daga cikin jami’o’in da ya kada a Najeriya, Farfesa Gwarzo ya ce cikin shekarar 2024, za a fara karatu gadangadan a wannan jami’a.
” Jami’an Canada za ta fara karatu daga shekarar 2024. Muna zangon karshe na kammala ayyuka a jami’ar domin soma karatu.
Farfesa Gwarzo ya kafa jami’o’i 4 a ƙasar nan da jamhuriyar Nijar wanda dukkan su suna aiki.
Discussion about this post