Jami’an SSS sun sake gurfanar da gogarman ‘yan Boko Haram, Husseni Ismaila, wanda ya tsara hare-haren luguden bama-bamai a masallacin Kano da kuma kan jami’an ‘yan sanda a 2012.
An sake gurfanar da Husseni wanda aka fi sani da suna Maitangaran a Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja a ranar Laraba.
Yayin da aka kira ƙarar, mai gabatar da ƙara E.A. Aduda, ya shaida wa kotu cewa SSS ta ƙara wasu canje-canjen da ta yi wa kwaskwarima guda hudu kan wanda ake ƙarar.
Ya nemi kotu ta karanta wa wanda ake ƙarar tuhume-tuhumen da ake masa, kuma ya yi wa kotu ba’asin da zai yi mata.
Wanda ake tuhumar dai ya musanta zargin da ake yi masa cewa, shi da kan sa ya ce shi ɗan Boko Haram ne, kuma a faifan bidiyon da SSS suka ɗauki bayanin sa, ya amsa cewa ya shiga cikin kai harin bama-bamai a Masallacin Sarki na Kano.
Mai gabatar da ƙara ya roƙi kotu ta ci gaba da shari’a, duk kuwa da cewa wanda ake zargin ya musanta aikata abin da ya aikata.
Sai dai kuma lauyan Maitangaran, wato Peter Dajang, ya ce bai kamata a ci gaba da shari’a ba, saboda mai gabatar da ƙara ya karya umarnin kotu.
Lauya Dajang ya ce a ranar 6 Ga Disamba, 2021, kotu ta umarci SSS su maida wanda ake tuhumar zuwa Kurkukun Kuje da ke Abuja.
Ya ce hakan zai sa lauyoyin sa da iyalan sa su samu damar ganawa da shi, amma har yau SSS ba su bi wannan umarnin ba. Ya ce har yanzu Maitangaran a hannun SSS ya ke.
Sai dai bayan lauyan SSS da lauyan Maitangaran sun yi cacar-bakin dogon Turanci, Mai Shari’a ya ɗage shari’ar zuwa 25 ga Janairu, 2024, inda zai yanke batun maida shi Kurkukun.
Discussion about this post