Wani matashi mai suna Olutimain Ilenre ya babbake takardun shaidar kammala karatunsa kaf na boko har da na yi wa kasa hidima a dalilin shekaru da ya yi yana neman aikin yi da su amma abin ya gagara.
Takardun da ya ƙona suna haɗa da na kammala yi wa kasa hidima NYSC, digiri, sakandare da sauran takardun sa tin daga Firamare.
Ilenre ya karanta kwas din tarihi da karatun kasa da kasa a Jami’ar Ajayi Crowther ya ce ya kona satifiket din na sa ne saboda ya yi shekaru 13 bai samu aikin yi ba.
Ya ce tun bayan da ya kammala karatunsa na jami’a lokacin yana dan samun aiki yana yi a dalilin sana’ar hannun da ya koya amma ba don karatun boko da ya yi ba.
“Na kammala karatun jami’a a shekarar 2010 kuma na yi bautanr kasa NYSC daga shekarar 2010 zuwa 2011 amma har yanzu ban samu aiki da takardu na ba.
“ A dalilin haka ya sa ban ga amfanin su ba kwatakwata, gara in babbake su kawai innsan ba zan yi amfani da su ba. Na fuskanci wani abin da ban ya fi min.
“Sannan kuma ko fita kayi da su kasashen waje, kawai takardun banza ake musu gani. Shawara ta ga iyaye shine a rika koya wa yara aikin hannu su samu sana’a shine kawai mafita. Idan abin ya gagara sai a koma sana’a.
Discussion about this post