Shekarar 2023 ta zo da labari maras daɗi a cikin Kannywood, inda a shekarar auren wasu faitattun ‘yan fim mata ya mutu.
Igiyar auren jaruma Zahara’u Shata, jikar marigayi Mamman Shata ta tsinke a 2023.
Haka ita ma Jaruma Hafsat Shehu, babbar yarinya mai shanawa, wadda ta auri ɗan-bana-bakwai, auren ta ya mutu a cikin 2023.
Sai kuma ta uku ita ce Wasila Isma’il, wadda tauraruwar ta ta yi haske sosai a farkon shekarun 2000, auren ta ya mutu, bayan shafe shekaru 21 a gidan miji.
Discussion about this post