An bayyana cewa Afrika, nahiya mai aƙalla ƙarfin arzikin albarkatun ƙasa har dala tiriliyan 6.2, nahiya mai kashi 65 bisa 100 na ƙasar noma a faɗin duniya tare da ɗimbin matasa majiya ƙarfi, to babu wani dalili ko uziri da za’a bayar a ce irin wannan nahiya ta dawwama cikin ƙangin talauci da fatara.
Shugaban Bankin Bunƙasa Ƙasashen Afrika, Akinwumi Adesina ne ya yi wannan furucin a ranar Talata.
Ya ce tilas Afirka ta tsaya ta yi wa kan ta karatun ta-natsu, ta nemo hanyoyin da za ta magance matsaloli da ƙalubalen da ‘yan nahiyar ke fuskanta.
Akinwumi ya ce a cikin nahiyar dukkan hanyoyin magance waɗannan matsaloli su ke, ba a waje can ƙasashen Turai, Amurka da Asiya ba.
Ya yi wannan kira a Legas, yayin da ya ke gabatar da lacca, a taron cikar jaridar The Guardian shekaru 40 da kafawa.
An gudanar da laccar mai taken Yadda Afrika Za Ta Yi Bunƙasar da Duniya Za Ta Yi Shakkar Ta.
Adesina, wanda shi ne Gwarzon Jaridar The Guardian na 2021, ya ce a gaskiya bai kamata a ce Afrika ta na matsayin da ta ke yanzu a duniya ba.
Kan haka ne ya yi kira manyan ƙasashe masu arziki na cikin nahiyar cewa su miƙe tsaye su ƙarfafa gwamnatin su, a riƙa shugabanci tsakani da Allah, kuma a riƙa kula da arzikin ƙasa, maimakon almubazzaranci da wawurar dukiya da suka yi ƙaurin suna a Gwamnatocin ƙasashen Afirka.
“Wato idan muka alkinta albarkatun ƙasa bil haƙƙi da gaskiya a Afrika, to Afrika ba ta wani uzirin da zai sa ta dawwama cikin fatara da talauci.”
Discussion about this post