Babban Bankin Najeriya, CBN ya bayyana cewa akwai isassun takardun kuɗi ɗankare a bankin da zai isa gudanar da hadahadar siye da siyarwa a Najeriya.
Bankin ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da Daraktan Sadarwa na Bankin Isa AbdulMumin ya sanyawa hannu a shafin X (wanda aka fi sani da Twitter) a ranar Alhamis.
” An jawo hankalin babban bankin Najeriya CBN kan rahotannin cewa wai ana fama da karancin takardun kudi a bankuna da na’rorin (ATMs), da kuma wuraren canji (BOGS) a wasu manyan biranen kasar nan. ”in ji sanarwar.
A dalilin haka haka muke kira ga ƴan Najeriya su kada su shiga cikin ruɗanin neman takardun kuɗi. Kowa ya kwabtar da hankalin shi, domin akwai isassun takardun kudi danƙare a babban bankin Najeriya.
CBN ya gano cewa an samu karancin takardun kudi a wasu birane ne saboda yadda mutane ke wafcan kudi daga bankuna babu ƙaƙautawa.
” Sai dai kuma duk da haka, muna so mu sanarwa ƴan Najeriya cewa kowa ya kwabtar da hankalinsa domin akwai isassun takardun kuɗi da zai isa mutanen kasa wajen hadahadar su na yau da kullum.
A ƙarshe bankin ya yi kira ga mutane su runguma harkar cinikayya ta hanyar biya ta yanar gizo da sauran hanyoyi da ba sai an rike takardar kuɗi ba.
Discussion about this post