Yayin da duniya ta maida hankali wajen shawo kan matsalolin canjin yanayi da ƙoƙarin komawa wajen sabbin dabarun amfani da makamashi wajen bunƙasa tattalin arziki, an bayyana cewa Najeriya da Afrika na buƙatar aƙalla tsakanin Dala Biliyan 22.6 zuwa Biliyan 30 a duk shekara, domin biyan buƙatar cike giɓin ratar makamashi.
Bayanin ya zo daidai lokacin da Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa za ta ci gaba da haɗin-guiwa da Bankin Musulunci wajen amfani da tsarin Sukuk domin jawo masu zuba jari na ciki da wajen Najeriya.
Wannan bayani ya fito ne a ranar Talata, yayin Taron Tsarin Hada-hadar Musulunci na Afrika (AICIF), wanda MTL da TMS suka shirya, tare da haɗin guiwar AFC da kuma Hukumar SEC.
Da ta ke magana a wurin taron, Shugaban Taro Ummahani Amin, ta bayyana cewa tsarin ci gaba daga mataki zuwa mataki na gaba ya na buƙatar samun kuɗaɗe ga ƙasashen Afrika masu fuskantar matsanancin canjin yanayi da ya ƙunshi yawaitar mace-mace, yawaitar raba ɗimbin jama’a daga muhallin su, yawaitar gudun hijira da sauran matsalolin da ke addabar yankunan Afrika.
Ummahani, wadda ita ce mai Kamfanin Lauyoyin Metropolitan Law Firm, wato MLF, ta nuna damuwa dangane da irin matsalolin rashin tsari ke ci gaba da addabar Afrika.
Daga cikin matsalolin da ta lissafa akwai yawan ciwo basussuka da ke zame wa ƙasashen alaƙaƙai, rashin sanin takamaimen yadda ake yi da kuɗaɗen da aka ciwo bashi ko kuma kuɗaɗen da ƙasashe ke samu na shiga da sauran matsaloli.
Shi kuwa Shugaban MSL ya yi tsinkayen cewa daga cikin Dala Biliyan 29.5 da Bankin AfDB ya bayar a Afrika domin bunƙasa hada-hadar 2019/2020, an yi amfani da kashi 32% bisa 100% ne wajen bunƙasa makamashi da inganta ilmin fannin makamashi da tsare-tsaren fannin makamashi ɗin, da suka haɗa da bunƙasa tashoshin samar da lantarki na cikin ruwa.
Shi kuwa Mataimakin Shugaban Ƙasa na Najeriya, Kashin Shettima, wanda Mashawarcin Shugaban Ƙasa kan Harkokin Tattalin Arziki, Tope Fasua ya wakilta, ya ce duk da irin damar da Bankin Musulunci ke da ita wajen ɗaukar nauyin jiɓintar harkokin tattalin, har yanzu tsarin tattalin arzikin bai rungumi tsarin tasarifin hada-hadar tsarin Bankin Musulunci ba.
Sai dai ya ce a yanzu Najeriya ta kama hanya kan bin wannan tafarkin hada-hadar tattalin arziki, ta hanyar faɗaɗa hanyoyin tsarin da ta ke bi, domin amfana da cin moroyar masu zuba jari masu zaman kan su.
Discussion about this post