Rundunar ‘yan sandan jihar Enugu ta bayyana cewa jami’anta sun kama wasu mutane uku da ake zargi da yi wa ‘yar shekara 3 fyade a jihar.
Rundunar ta ce yarinyar dalibar makarantar mai zaman kansa ne mai suna ‘Tenderlink School Trans-Ekulu’ dake jihar.
Kakakin rundunar Daniel Ndukwe ya sanar da haka a ƙarshen makon jiha.
Ndukwe ya ce malamar makarantar, direban motar ɗaukar yaran makaranta da wanda ke kula da dalibai ne ake tuhuma da laifin aikata wannan mummunar abu.
Ya ce dakarun sun kama wadannan mutane bayan an ga jini a gaban yarinyar lokacin da ta dawo daga makaranta ranar Talatan makon jiya.
Ndukwe ya ce gwamnati ta rufe makarantar bayan ta samu labarin abinda ya faru daga iyayen yarinyar cewa ana yi wa ‘ya’yan mutane fyaɗe a wannan makaranta.
Ya ce gwamnati ta bai wa kwamishinan ‘yan sandan jihar Kanayo Uzuegbu umarnin gudanar da bincike domin kamowa da hukunta wadanda ke da hannu a aikata wannan mummunar abu.
Discussion about this post