Gwamnan jihar Neja Umar Bago, ya bayyana cewa wasu ƴan kasuwan kasar Saudiyya za su gyara titin Minna-Bida nan ba da daɗewa.
Wannan titi ya ragwargwaɓe da ya kai ga ba a iya bin shi cikin kwanciyar hankali ,sannan kuma gwamnatocin baya ba su iya gyara shi ba.
Gwamna Bago ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da manema labarai a lokacin wata zama da aka gudanar a Makka, tare da wasu jigajigan yan kasuwan kasar Saudiyya karkashin jagorancin Shugaba Bola Tinubu a ranar Litinin.
Bago ya ce wasu daga cikin masu zuba jari ƴan kasar Saudiyya sun bayyana aniyarsu ta zuba jari a ayyukan noma da samar da ababen more rayuwa a fadin jihar.
Bago ya ce tattaunawar da aka yi da Saudiyyar ta hada da gyara hanyar Minna zuwa Bida.
Ya ce masu zuba jarin sun zabi jihar Neja ne domin gwaji na harkar noma saboda kusancin da take da babban birnin tarayya da kuma wadarar ruwan noma.
“Muna da madatsun ruwa guda hudu da suke aiki a halin yanzu sannan muna da kogin Neja da kogin Benuwai duk ratsa ta jihar mu.
“Mu ne kan gaba wajen noman Sheanut da kuma shinkafa a Najeriya.
“Don haka, wannan wata dama ce da kuma hanyar nuna kanmu, wanda muka yi.
Discussion about this post