Gwamna Ademola Adeleke na Jihar Osun, ya umarci ilahirin ma’aikatan jihar su riƙa yin shigar anko na ɗinkin zanin adire zuwa wurin aiki.
Ya ce su riƙa yin haka aƙalla sau ɗaya a kowane mako, don haka sai aka ware ranar Laraba matsayin ranar shigar anko.
Umarnin ya na ƙunshe cikin wata sanarwar da Shugaban Ma’aikatan Jihar Osun, Ayanleye Aina ya fitar a ranar Alhamis, a Osogbo, babban birnin jihar.
Wannan umarnin ya rataya a wuyan dukkan ma’aikacin jihar a kowace ma’ikata, hukumomi da cibiyoyin gwamnati.
Haka nan kuma umarnin ya shafi dukkan makarantun gaba da sakandare na jihar, ƙananan hukumomi da ofisoshin yanki.
“Daga yau kowace Laraba ana so a fito cikin anko na kayan adire, a Matsayin Ranar Ankon Adire.
“Kuma umarnin ya haɗa har da duk wani mai riƙe da muƙamin siyasa, tun daga kwamishinoni da sauran masu duk wani muƙamin siyasa.”
Sanarwar ta ce a Gwamna Adeleke ya gabatar da buƙatar anko ɗin Adire a gaban Majalisar Zartaswa, kuma aka amince.
Ya ce Adire tufafi ne na al’adar Yarabawa, wanda ya samo tushe da asali daga Jihar Osun.
Discussion about this post