Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Mohammed Idris, ya nuna damuwar sa ganin yadda akasarin ‘yan Najeriya sun daina yin amanna, yarda ko gaskata kalaman da ke fitowa daga bakin shugabannin su.
Ministan ya bayyana haka a wata tattaunawa da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN), a Abuja.
“Abin da mu ke so shi ne a bar ‘yan Najeriya su san gaskiya daga waɗanda suka wajaba su bayyana masu gaskiyar. Ina ganin muhimmin abu ne sosai a ga cewa an ɗora tsarin isar da saƙo a kan turbar faɗa ko bayyana gaskiya, ta yadda wanda ake faɗa wa gaskiyar zai yi amanna da abin da mai faɗa masa gaskiyar ya ke faɗa.
“Wannan haka ne, saboda mun ga irin yadda amanna da gwamnati da kuma amincewa suka gushe ko suka zaizaye a zukatan jama’a, a ƙasar nan.
“Mun kai matakin da akasarin ‘yan Najeriya ba su yin amanna da abin da shugabannin su ke faɗa masu. Kuma fa su mutanen su suka zaɓi shugabannin da hannun su.
“Saboda haka akwai matuƙar buƙatar mu fara ganin mun kankaro wannan gwamnati daraja, ta hanyar samun amincewa da amanna daga wurin ‘yan Najeriya.
“Za mu yi wannan aikin haiƙan, bakin ƙarfi da iyawar gwamnati, domin ganin jama’a sun dawo su na gaskata kalaman da bayanan gwamnati,” cewar Idris.
Ya ƙara da cewa faɗin gaskiya shi ne matakin farko na nagartar mutum, domin idan jama’a suka san gwamnati na faɗar gaskiya, to su ma fa masu bada rahotannin bayanai tsakanin tilas su riƙa faɗar gaskiya.
Idris ya ce gwamnati na ƙoƙarin ƙara zaburar da jama’a cewa ko wa ya kasance ya na faɗar gaskiya.
“Za mu fito mu yi kamfe na daƙile masu yaɗa labaran bogi da ƙarairayi, waɗanda hatsarin su zai iya kaiwa ga ruguza al’umma ko kawo rabuwar kai.
“Kuma za mu ci gaba da kwaɗaitar da kafafen yaɗa labarai su tsaya kan turbar bayyana gaskiya, wadda dama ita ce kyakkyawar ɗabi’ar da aka san kafafen yaɗa labarai ke kan ta, kuma suke kan koyarwar ta,” cewar Minista Idris.
Dangane da labaran bogi, Idris ya ce wannan matsala ba ta Najeriya kaɗai ba ce, abu ne wanda ya game duniya. Ya ce idan aka haɗa hannu za a iya kawar da yaɗuwar su, ba tare da an take haƙƙin kowa ba.
Discussion about this post