Mai magana da yawun Shugaban mayakan Hamas, Abu Obeida ya bayyana cewa daga yanzu haka idan Isra’la ta ci gaba da kai wa mutanen da basu ji ba basu gani ba hari suna kashe mata da yara, za su rika kashe ‘yan Isra’ila da suka kama daya bayan daya har sai sun gama da su.
Obeida ya ce ba kashe su kawai za su rika yi ba, za su rika nuna yadda suke kashe su.
” Za mu rika kashe bayin da muka kama ‘yan Isra’ila daya bayan daya hjar sai mun gama da su daga yau, idan har Isra’ila ba ta daina yi wa mutanen mu a Gaza luguden wuta ba”
Har yanzu ana ci gaba da yi wa Gaza ruwan bamabamai daga sama babu kakkautawa.
Luguden Bamabamai a Gaza
Isra’la na cigaba da yi wa yankin Gaza luguden bamabamai a cigaba da yaki da ta ke yi da Hamas a yankin Gaza.
Zuwa yanzu rahotanni sun nuna cewa akalla mutum 570 ne Palastinawa suka rasu a harin da suke kaiwa. Yan kasar Isra’ila 800 suka rasu zuwa yanzu.
Sai dai kuma Isra’la ta fusata matuka domin ta umarci dakarunta akalla 300,000 su daura damaran yaki su jira aba su oda su shiga Gaza su fafata da Hamas.
Isra’la ta fusa ta ne bayan yan kungiyar Hamas sun far wa wani garin Yahudawa inda suka kashe mutum sama da 200, sannan suka yi garkuwa da mutane, mata da yara ma su yawan gaske.
Jiragen Isra’ila na ci gaba da luguden wuta a Gaza babu kakkautawa. Haka suma yan Hamas suna ci gaba da harba bamabamai a yankin Isra’ila babu kakkautawa.
Discussion about this post