Hukumar NiMet ta bayyana cewa wasu jihohi za su rika samun manyan ruwan sama daga ranar Talata zuwa Alhamis a kasar nan.
Jihohin sun haɗa da Kebbi, Niger, Kwara, Oyo, Ogun, Osun, Ekiti, Ondo, Delta, Bayelsa, Imo, Abia, Akwa Ibom, Cross River, Benue, Taraba, Adamawa da Borno na daga cikin jihohin da za a rika yi musu ruwa kamar da bakin kwarya.
Hukumar ta ce a dalilin ruwan saman da za a rika samu za a yi fama da zaizayar kasa, ambaliyar ruwa, barkewar cututtuka da dai sauran su.
NiMet ta yi kira ga gwamnati da ta dauki matakan da za su taimaka wajen kare rayuka da dukiyoyin mutane daga wannan ibtila’in da zai iya faruwa.
Daga nan hukumar ta ce jihohin Filato, Bauchi, Kwara, Oyo, Osun, Ekiti, Edo, Kogi, Nasarawa, Imo, Abia, Akwa Ibom, Cross River, Taraba da babban birnin tarayya Abuja za su rika samu yayyafi a tsakanin wannan lokaci.
NiMet ta ce jihohin Kwara, Oyo, Ogun, Legas, Edo, Delta, Bayelsa, Kogi, Adamawa da Abuja za su rika samun matsakaicin ruwan sama daga ranar Laraba.
Sannan daga ranar Alhamis jihohin Oyo, Ogun, Lagos, Osun, Ekiti, Kogi, Kaduna, Nasarawa, Filato, Edo, Delta, Bayelsa, Rivers, Anambra, Rivers, Imo, Abia, Akwa Ibom, Enugu, Ebonyi, Cross River, Benue, Taraba, Adamawa da FCT za su rika samun matsakaicin ruwan sama.
Bayan haka hukumar ta ce a dalilin canjin yanayin da za a rika samu daga Talata zuwa Alhamis wasu bangarorin kasar za su rika fama da guguwar iska mai ƙarfi.
NiMet ta ce Nan da kwanaki uku musamman a ranar Alhamis jihohin Katsina, Kano, Jigawa, Bauchi, Gombe, Yobe da Borno, Sokoto, Zamfara, Kaduna, Kogi, Nasarawa, Niger, Filato, Adamawa da FCT za a samu iska mai karfi.
Discussion about this post