Wata mata mai suna Nana Ado ta taimaka wa jami’an tsaro wajen kama mutumin da ya yi garkuwa da ‘yarta a Zariya.
Wani majiya ya shaida wa ‘Daily Post’ cewa wani Aminu Ibrahim mai shekara 35 ya kashe Fatima Ado mai shekara 23 bayan ya yi garkuwa da ita a Zaria kuma ya birne ta a gidansa dake layin Limancin Iya a Zaria.
Kanwar mahaifiyar Fatima, Hajara Adamu ta yi bayanin cewa Ibrahim kan yi wa Fatima dinkin kaya. Ranar da ta fice daga gida a Wusasa mun sani cewa Kaduna zata.
“ Mun yi ta kokarin mu same ta a waya amma baya shiga. Daga baya dai sai aka kira mu aka ce wai an yi garkuwa da ita mu kawo naira 100,000 kudin fansa.
” Haka dai muka kukkuta aka haɗa naira 100 ,000 da kyar aka aika masa. Sai dai bayan ya amshi kuɗin sai ya ce ba zai sake ta sai an ƙara nata naira 100,000.
Hajara ta ce sai da Nana ta siyar da fili sannan ta samu naira 100,000 da masu garkuwan ke bukata.
Da Hajara ta haɗa naira 100,000 ta kai inda aka ce ta kai, sai ta gane mai karɓarkuɗin ashe telar Fatima ne Ibrahim ya yi garkuwa da ita.
Daga nan sai ta kwala ihu tana kiran jama’a, haka dai aka kama shi.
A hannun ‘yan sandan a Dan Magaji Zaria Ibrahim ya tabbatar cewa shine ya yi garkuwa da Fatima amma ta rasu yayin da take tsare a hannunsa.
Ibrahim ya nuna wa ƴan sanda inda ya birne Fatima a gidan sa.
Ibrahim ya kuma ce su biyar ne suka yi garkuwa da yarinyar inda zuwa yanzu ‘yan sanda sun kama mutum biyu suna farautar sauran mutum biyu.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Mansir Hassan ya tabbatar da haka yana mai cewa da zarar an kammala bincike za a kai wadannan mutane kotu.
Discussion about this post